More Podcasts
Akan ce ‘Noma tushen arziƙi’ kuma mutane da dama za su iya bayar da labarin da ke tabbatar da hakan; domin kuwa ko ba komai idan mutum ya samu abinci ya ci ya ƙoshi babban arziƙi ne.
Wasu ’yan Najeriya kan shuka kayan abinci a unguwanninsu don sama wa kansu abincin da za su ci.
Sai dai masana na ganin da waɗannan mutane za su inganta wannan noma da sun sama wa kansu kuɗaɗen shiga.
- NAJERIYA A YAU: Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Intanet
- DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a?
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan hanyoyin da ’yan Najeriya za su iya bi don sama wa kansu kuɗaɗen shiga bayan sun noma abin da za su ci.
Domin sauke shirin, latsa nan