Shugaba Muhammadu Buhari ya ce halin da ’yan Najeriya suka tsinci kansu a ciki yana ba shi tausayi.
Ya kuma roki malaman jami’o’in gwamnati da su janye yajin aikin da suka shafe wata bakwai a ciki, a jawabinsa na gayowar ranar samun ’yancin kasar a safiyar Asabar.
- Nigeria@62: Yadda matsalolin tsaron Najeriya za su iya zama tarihi – Masana
- Yadda manoma 14 suka rasu a hatsarin kwalekwale a Taraba
Shugaban kasar ya ce, “Na damu da damuwar ‘yan Najeriya kuma in tabbatar muku cewa hakurinku da juriyarka ba sai tafi a banza ba.
“Gwamnatinmu na ci gaba da yin abin da ya dace wajen karfara hukumomin tsaro domin su shawo kan duk nau’ikan matsalolin tsaro.”
Ya ci gaba da cewa, “Na damu matuka kan tsaikon da aka samu a bangaren ilimin musamman rufe manyan makarantu.
“Don haka ina rokon malaman jami’o’in su mai da wukarsu cikin kube su koma bakin aiki, sannan su ci gaba da tattaunawa domin daidaita al’amura tsakanin bangarorin.”
A jawabin nasa wanda shi ne na karshe a irin wannan rana yana shugaban kasa, Buhari ya yi roki ’yan siyasa da jam’iyyu da su guji duk wani abu da zai kawo matsala ga zaben 2023, domin a mika mulki ga gwamnati mai zuwa cikin kwanciyar hankali.
Ya kuma yi kira ga mata da matasa da su shiga a dama da su sosai a zaben da ke tafe.
“Ina fata matasanmu sun fahimci cewa tashin hankali babu abin da yake kawowa sai matsala ga zabe.
“Ina fata ba za su bari a yi amfani da su a wurin bangar siyasa ba a nan gaba,” in ji shi.
Buhari ya fara jawabin ne da godiya ga ’yan Najeriya bisa hakurin da suka yi da kamun ludayin gwamnatinnsa a tsawon lokaci.
“Kun yi hakuri da yunkurinmu da kura-kuranmu da kuma nasarorin da muka samu,” in ji shi.
Ya bayyana cewa duk da matsalolin da suka yi wa Najeriya tarnaki, gwamantinsa ta samun nasara a bangarori da dama, duk da cewa haka ba ta gama cim-ma ruwa ba.
“Daya daga cikin bangarorin da muka yi nasara shi ne bangaren yaki da almundahana da ta yi katutu a Najeriya.
“Mun karfafa hukumomin yaki da rashawa wanda ya kai ga tsare manyan masu laifi da kuma dawo da makudan kudade da aka sace mana aka kai aka boye a kasashen waje.”
Ya ci gaba da cewa a bangaren tsaro, “Mun yi aiki haikan domin dankwafe ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, muna kuma kokarin gamawa da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.”
Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi kokarin fita sau biyu daga matsin tattalin arziki.