✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya @62: Jawabin Buhari ga ’yan Najeriya a takaice

Buhari ya tabo batutuwa da dama musamman irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu kawo yanzu.

A ranar Asabar Shugaba Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi jawabinsa na karshe na zagayowar ranar samun ’yancin Najeriya ga ’yan kasar yana kan mulki.

A jawabin nasa da aka yada kai-tsaye a kafafen yada labarai, Shugaba Buhari ya tabo batutuwa da dama musamman irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu kawo yanzu.

Ga wasu daga cikin abubuwan da Aminiya ta kalato daga jawabin:

  • Godiya da yabo ga Allah da kuma ’yan Najeriya bisa ba shi damar mulkin kasa.
  • Ya yi waiwayen alkawarinsa na inganta tsaro da tattalin arziki da yaki da rashawa.
  • Ya ce gwamnatinsa ta karfarfa hukumomin yaki da rashawa.
  • Ta toshe kofoffin sace dukiyar kasa ta kuma kwato wadda aka sace aka boye a ketare.
  • Ta karya lagon ’yan ta’dda a yankin Arewa maso Gabas da kuma Neja Delta.
  • Ta bunkasa fannin noma wanda ya samar da ayyuka ga dimbin ’yan kasa.
  • Ya ba da tabbacin hakuri da juriyar da ’yan kasa suka nuna ba za su tafi banza ba.
  • Gwamnati za ta ci gaba da karfafa fannin tsaro har sai an cim-ma cikakkiyar nasara.
  • Ya roki malaman jami’a su janye yajin aiki tare da tabbatar musu gwamnati za yi kokarin biyan bukatunta.
  • Ya ce gwamnatinsa ta yi bunkasa fannin lafiya, musamman a lokacin da bayan bullar COVID-19.
  • Ta fadada hanyoyin tara kudaden shiga don inganta tattalin arzkin kasa.
  • Ta yi shirye-shiryen tallafin kyautata rayuwar talakawa, kamar N-Power, Trader Money, Market Money da sauransu.
  • Ya ce sai da tsarin zabe mai inganci Najeriya za ta samu cigaban da take bukata.
  • Yi yi Kira ga mata da matasa su shiga a dama da su a harkokin siyasa.
  • Kira ga ’yan siyasa su guji haifar da tashin-tashina yayin neman zabe da dai sauransu.