A ranar Asabar Shugaba Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi jawabinsa na karshe na zagayowar ranar samun ’yancin Najeriya ga ’yan kasar yana kan mulki.
A jawabin nasa da aka yada kai-tsaye a kafafen yada labarai, Shugaba Buhari ya tabo batutuwa da dama musamman irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu kawo yanzu.
Ga wasu daga cikin abubuwan da Aminiya ta kalato daga jawabin:
- Godiya da yabo ga Allah da kuma ’yan Najeriya bisa ba shi damar mulkin kasa.
- Ya yi waiwayen alkawarinsa na inganta tsaro da tattalin arziki da yaki da rashawa.
- Ya ce gwamnatinsa ta karfarfa hukumomin yaki da rashawa.
- Ta toshe kofoffin sace dukiyar kasa ta kuma kwato wadda aka sace aka boye a ketare.
- Ta karya lagon ’yan ta’dda a yankin Arewa maso Gabas da kuma Neja Delta.
- Ta bunkasa fannin noma wanda ya samar da ayyuka ga dimbin ’yan kasa.
- Ya ba da tabbacin hakuri da juriyar da ’yan kasa suka nuna ba za su tafi banza ba.
- Gwamnati za ta ci gaba da karfafa fannin tsaro har sai an cim-ma cikakkiyar nasara.
- Ya roki malaman jami’a su janye yajin aiki tare da tabbatar musu gwamnati za yi kokarin biyan bukatunta.
- Ya ce gwamnatinsa ta yi bunkasa fannin lafiya, musamman a lokacin da bayan bullar COVID-19.
- Ta fadada hanyoyin tara kudaden shiga don inganta tattalin arzkin kasa.
- Ta yi shirye-shiryen tallafin kyautata rayuwar talakawa, kamar N-Power, Trader Money, Market Money da sauransu.
- Ya ce sai da tsarin zabe mai inganci Najeriya za ta samu cigaban da take bukata.
- Yi yi Kira ga mata da matasa su shiga a dama da su a harkokin siyasa.
- Kira ga ’yan siyasa su guji haifar da tashin-tashina yayin neman zabe da dai sauransu.