✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Naira ta fadi warwas, ’yan sisaya na neman ta ido rufe

Dala ta kai N595 saboda yadda ’yan siyasa masu neman takara ke neman tara ta a gigice gabanin zaben fid-da gwani

A yayin da ’yan siyasa suka dukufa sayen Dala gabanin zaben fitar da ’yan takarar jam’iyyu na zaben 2023, a yanzu haka darajar Naira ta kara karyewa.

Binciken Aminiya ya gano cewa a ranar Alhamis ta yi tashin gwauron zabon da ba ta taba yi ba zuwa Naira 595, a kasuwar bayan fage, wadda a wata biyu kafin nan farashin Dala ya tashi daga Naira 550 zuwa Naira 570.

Farashin Dala da Babban Bankin Najeriya (CBN), ya kayyade shi ne N415, kuma bankin babu ruwansa da kasuwar canji ta bayan fage

Binciken wakilanmu ya gano darar Naira na ta kara karyewa a kasuwar canji ta bayan fage, sakamakon yadda mutane ke ta tururuwar zuwa neman kudaden kasar waje.

Mun gano cewa Data ta fara karanci a wadansu bankunan kasuwanci ta yadda za su iya biyan bukatun kwastomomin da ke nema.

Wannan lamari dai ya haifar da fargabar cewa Dala na iya tashi ta kai N600, saboda karancin nata.

’Yan siyasa na neman Dala ido rufe

Yadda ’yan siyasa masu neman takara ke neman Dala a haukace, gabanin zaben fitar da ’yan takarar jam’iyyunsu ya yi tasiri wajen kawo karanci da kuma tashinta.

’Yan canji sun shaida wa wakilanmu cewa ’yan siyasa na amfani da yaransu, suna sayen kudaden kasar waje.

A yayin da masu neman takarar ke kokarin saye zukatan daliget din da za su yi zaben fitar da ’yan takara, ana ganin daukar kudaden kasar waje ta fi saukin da kuma kwarjini, musamman Dala — maimakon yawo da manyan jakunkunan Naira.

A ranar 28 zuwa 29 ne dai babbar jam’iyyar adawa ta PDP za ta gudanar da zaben fitar da dan takarar shugaban kasarta, inda mutum 15 da ke zawarcin kujerar za su fafata.

Jam’iyyar APC mai mulki kuma ta sanya ranar 30 da 31 domin gudanar da zaben fitar da dan takararta cikin kusan mutum 30 da suka sayi fom.

Bincikenmu ya gano cewa tun kimanin mako biyu da suka gabata masu neman takara a PDP da APC ke karade sassan Najeriya suna sayen Dala.

Daliget 7,800 ne dai zai jefa kuri’a a zaben dan takarar APC, na PDP kuma mutum 3,700.

Tun a makon jiya Aminiya ta gano daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a APC yana raba wa kowane daliget tsakanin Dala 300 (N178,500) zuwa Dala 400 (N238,000) a wasu jihohi biyu da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Wani tsohon gwamnan da muka yi hira da shi ya shaida mana cewa wata shugaban hukumar gwamnatin tarayya da ke kan gaba wajen tallata wani dan takarar gwamna ce kan gaba wajen tara kudaden kasar wajen.

Ya ce, “Tana cikin manyan wadanda da suka kawo karancin Dala, ita ke sa a sayo; za a samu tashin Dala, saboda miliyoyin Dala take saye.”

Wakilanmu sun gano ba a tsakanin masu neman takarar shugaban kasa wannan salo na tara Daloli ya takaita ba, har da masu neman kurar gwamna da majalisa dokoki.

Baya ga daliget, masu neman kujerun na kuma kokarin samun goyon baya da saye zukatan masu fada a ji a harkokin siyasa, ciki har da sarakunan gargajiya da shugabannin addini da jami’an tsaro da kungiyoyin farar hula da sauransu.

Karin Dala ta yi kamari

Zuwa ranar Alhamis da ana sayar da Dala N595 a kasuwar bayan fage da ke Filin Jirgi na Muratala Mohammed da sauran wurare da ke Legas, inda yawancin ’yan canji ke sayar da ita tsakanin N585 zuwa N595.

“Idan ka je banki, iya abin da za ka samu bai wuc Dala 2,000 ba,” inji wani dan canji a layin Allen Avenue da ke Legas, mai suna Nasiru.

Ya zargi babban bankin da bai  wa mukarabbansa ’yan siyasa canjin Dala.

A Abuja kuma ana sayar canjin Dala a kan N591 zuwa N591, inda ’yan canji suka ce yadda ake namen ta a watan Afrilu ya karu sosai, amma ya ragu a cikin watan Mayu.

A kasuwar ’yan canji ta Wapa da ke Kano, Aminiya ta same su suna gudanar da harkokinsu yadda suka saba, amma babu alamar hadahadar Dala.

Daya daga cikin ’yan canjin da muka tattauna da su ya ce farashin Dala na ta karuwa a cikin kwanakin nan.

“Kimanin mako daya zuwa biyu da suka gabata N585 zuwa  N587 muke sayarwa, amman kwatsam ta tashi zuwa N591 a makon nan, to ka duba wannan karin,” inji shi.

Shugaban Kungiyar ’Yan Canji ta Najeriya, Alhaji Aminu Gwadabe ya danganta tashin Dalar da kuma karancinta da ’yadda ’yan siyasa ke neman ta, duba da yawan masu neman takarar shugaban kasa a zaben 2023.

 

Daga: Sagir Kano Saleh, Ismail Mudashir, Chris Agabi (Abuja), Clement A. Oloyede, Zahraddeen Y. Shuaibu (Kano) & Abdullateef Aliyu (Legas).