“Na Kankiya Malan Ado,
Kai mu matso mu ga Malan Ado,
Na Kankiya Malan Ado.
Garin Kankiya za ni je wasa,
ga na Kankiya Malan Ado,
Na Kankiya Malan Ado.
Malam Ado Kankiya na daya daga cikin malaman makarantar boko da marigayi Dokta Mamman Shata ya yi wa waka. dan asalin garin Katsina, haifaffen garin Kankiya, ya yi suna a harkar malanta, kuma Aminiya ta gana da shi a gidansa da ke Unguwar Tudun Wada a cikin garin Katsina domin jin yadda suka hadu da marigayi Mamman Shata har ya yi masa waka:
Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?
Ado Kankiya: Sunana Ado Kankiya mazaunin Katsina, da kuka ji ana kirana Ado Kankiya an haife ni a garin Kankiya a 1938. Na yi firamare a Kankiya lokacin ana yin jarrabawar zuwa makarantar gaba (common entarance). Sai kanen mahaifiyata ya zo daga Daudawa ya tafi da ni, aka mayar da ni makarantar Daudawa a 1957. Bayan shekara daya sai na ji cewa na ci waccan jarrabawa ta kwaman intaras, sai aka kawo babbar firamare ta Funtuwa a 1958. Na gama wannan makaranta ta Funtuwa a 1960 inda aka kawo ni wata makaranta sabuwa da aka bude da ke garin Dutsinma ana kiranta post primary. Mun shekara daya sai aka yi mana jarrabawa muka taho Kwalejin Koyon Malanta ta Katsina (KTC) a 1962. Mun yi shekara biyar a nan KTC, a nan makarantar an rarraba mu kashi uku, ajin A da B da C. To sai aka ce ajin A da B za su yi shekara biyar don yin karatun takardar shaida mai daraja ta biyu (Grade II). Su kuma ’yan ajin C za su yi karatun mai daraja ta uku. Bisa kaddara sai sunana ya fada cikin ajin C. Farko na hakura a kan haka, amma sai na yi ta tunani a kan irin yadda na ga an fiddo wani Mudi Hassan dan gidan Sarkin Yaki da Aminu Abubakar Tafawa balewa wadanda muke aji daya da su amma saboda suna ’ya’yan wasu sai aka ce su koma can wajen yin karatun Grade II. Kawai sai na rubuta takadar korafi na aika wa Ministan Ilimi, lokacin Marigayi Isa Kaita ne, sai Iro Safana (yana nan da ransa) yana Sakatarensa mai zaman kansa. Aka yi sa’a Ministan zai zo Katsina da ya zo sai ya je makarantarmu. Lokacin da ya shigo ajinmu a cikin zagayen da ya yi, bayan ya gama yi mana fada har ya juya zai fita, sai suka tsaya bakin kofa shi da Iro Safana, suka yi magana sai shi Ministan ya ce, “wane ne Ado Kankiya?” Sai na tashi tsaye na ce, “ga ni.” Bai ce mini komai ba bayan ya ce in zauna. To nan fa hankalina ya tashi na fara tunanin ko kora ta za a yi. Sai kuma na yanke shawarar bari in bi shi gida in ji domin ba ni so a zo cikin mutane a ce an kore ni. Ka ga in na ji cewa an kore ni, to babu mai sanin tafiyata. To lokacin da na zo gidansa sai na hadu da kakana marigayi Alhaji Mamman Kankiya ya fito daga wajen shi Ministan. Koda ya gan ni ya tambaye ni abin da ya kawo ni, na ba shi labarin abin da ya faru na ya shigo ajinmu ya tada ni kuma bai ce mini komai ba, shi ya sa na zo inji dalili. Sai ya ce da dai ya yi ban-kwana amma in zo mu je. Bayan mun shiga ya shaida wa Minista dalilin dawowarsa tare da ni sai Minista ya ce, “na je na bincika fayil naka na ga kana da kokari, kai ma za ka je ka yi Grade II, amma kada ka gaya wa kowa ka bari har sai kun gama Grade III sai ka dawo ka shiga cikin sauran ’yan ajinku ku ci gaba. To ina gama Grade III sai aka tura ni Doro wajen marigayi Iro ’Yar’aduwa. Da na je sai naga gidan da zan zauna babu darni (marfin kofa) sai na ce, ban zama. Na zo na samu babban jami’in ilimi Alhaji Rabi’u Abdullahi na ce a sake mini waje shi kuma ya ce ba zai canja ba, sai dai in bari, ni kuma na ce, na bari. Sai na zo na shaida wa Alhaji Musa ’Yar’aduwa lokacin yana Minista na kuma tafi wajen Sarkin Fada Damale na shaida masa. karshe dai aka tura ni Daudawa bayan an sake mayar da ni can wajen shi wanda ya tura ni Doro na ce ban zama. To, ina shirin tafiya Daudawa sai ga takarda daga ofishin Ministan Ilimi Isa Kaita cewa in je in shiga wancan aji in ci gaba, kawai sai makaranta, lokacin da na samu shugaban makarantar ya so jin alakata da Minista. Don in kara samun shiga sai na ce, “He is the elder brother of my father.” (Yayan mahaifina ne). To, bayan mun gama wannan karatun sai aka sake tura ni can dai Daudawar, daga Daudawa sai aka tura ni zuwa makarantar Aya da ke Funtuwa a 1967.
Aminiya: To yaya kuka hadu da shi Shata har ya yi maka waka?
Ado Kankiya: A nan makarantar Aya ne na fara haduwa da shi Shata. Abin da ya faru kuma shi ne, Hedimasta baya nan sai nake rike da makarantar. Shata ya shigo makarantar yana nemansa, sai aka ce baya nan sai dai mataimakinsa. Aka je filin kwallo inda nake wasa da wasu dalibai aka ce in zo Shata na nemana. To dama ban taba ganinsa ba, nan da nan na zo. Sai ya ce, kara ya kawo. Na ce, ta wa? Ya ce ta su Lawal dana, domin a gida mata sun gaya mini cewa a duk lokacin da aka tado su daga makaranta ba su zuwa gida sai su tafi gidan Hedimasta shi ya sa ya kawo kara. Na ce, eh haka ne. Amma ka tambaye su, ba ni sanya su shara ko daukar ruwa, karatu nake koya musu tare da ’ya’yan da na haifa. Nan take ya nuna jin dadinsa ya kuma ce zai koma gida ya yi musu bayani. Sai ya kawo fam daya ya ba ni, ni kuma sai na juya na mika wa wata malama daga cikin malaman da suka biyo mu zuwa ofis na ce su raba nan gabansa. Sai ya jinjina kai ya ce, “lallai kai dattijo ne. Na ba ka abu kai kuma ka ba na kasanka? To bari in ba ka wata.” Na amsa na yi godiya. Ban sake haduwa da Mamman Shata ba, tun daga wannan lokaci har aka dauke ni daga Funtuwa aka kawo ni Guga kasar Bakori. Zuwana nan yaran suka fara cin jarrabawa wadda hakan ya ja har aka yi mini kyauta ta Fam biyar wadda Sarkin Katsina Usman Nagogo ya ba ni a nan makarantar Aya inda aka yi taron ba ni wannan kyauta. To daga nan fa sai aka rika kai ni makarantu daban-daban inda ake samun matsala don in yi gyara. A dandume na samu matsala da Hedimastan da aka tura ni in canja wanda kuma yake dan ajinmu ne. Sai dai ya ce, wai an karo masa malami maimakon ya fadi cewa ni ne Hedimasta. Da na ga haka sai na dawo Funtuwa wajen Alhaji Garba Sarkin Malamai na shaida masa abin da ya faru. Shi da kansa ya je ya tabbatar musu da cewa ni ne ba wancan ba. A 1972 sai kuma aka ce za a kai ni Sabuwa makarantar ta lalace. Nan ne nac e wai ni sai inda aka samu matsala ake kai ni?
Da yin hutu sai na tafi Kaduna inda muka hadu da Alhaji Sule Idris Makaman Katsina wanda shi ma dan ajinmu ne. Na gaya masa cewa zan canja aiki daga malanta. Cikin sa’a ya ce, ka zo a daidai, gobe za ka je wajen jarrabawar da za a yi ta ma’aikatan da za su kula da aikin Dala. Daga cikin mu 340 sunana ne na uku. To sai aka rarraba mu inda ni aka kawo ni Funtuwa inda muka yi kwas a cikin wannan shekara ta 1972 a nan ne ma na yi wannan hoton mai hular da ake kira Hana-Sallah. Bayan mun gama kwas sai aka turo ni nan Katsina inda na ci gaba da wannan aiki har na tsawon shekara biyar. karshe dai kuma sai na sake komawa wancan layi na koyarwa da na bari. Sai kuma bude makarantu da kuma karin ci gaba har na zama Baturen Makaranta mai kula da Kaita da Jibiya a 1977 kuma a lokacin ne na ji sanarwa ana cewa Shata zai yi wasa a kulob din Nasara a cikin garin Katsina. Jin haka sai na nufi inda ya sauka gidan Alhaji Shehu Shema, zuwana sai na yi kicibis da Wazirinsa wanda dama ya san ni, sai ya sa aka shiga aka gaya masa ga Ado Kankiya nan ya zo wajensa. Amma fa shi Shata ya mance ni, da na shiga bayan na gaishe shi, sai ya dube ni ya ce, “Ni kuwa na so in san ka sai dai na mance ko ina ne?” Nan fa na tuna masa da inda muka hadu. Bayan da ya tuna ya kuma shaida mini cewa zai yi wasa, ya tambaye ni ko zan zo. To da zan fito sai na kira marigayi Alhaji Shehu Tsatso na ba shi Fam biyar na ce ya ba Shata. Lokacin da nake kokarin sallamar su Waziri sai ga shi ya fito ya yi mini godiya bayan ya ji cewa ni na bada a ba shi. To a nan ne ya ce mini in na zo wajen wasan in ba shi Shehu Tsatso Naira ya ba shi yace inji Ado Kankiya don ya tuna, haka kuma aka yi. Hakan kuma ta sa mutane suka rika cewa, “Naira daya na ba Shata ya yi mini waka.” Nan ne ya fara wakar, “Malan Ado Kankiya.”
Aminiya: To a cikin wakar wadanne baitoci ne suka fi burge ka?
Ado Kankiya: Abin da ya burge ni shi ne, ni dai ban gaya masa sunayen matana ba balle na ’ya’ya amma sai kawai na ji yana ambato su. Muna zaune ni da Sa’i muna sauraren wakokin, in ya yi tawa sai ya yi ta Sa’i. Wata rana kawai sai na ji wakar tawa an sanyo ta daga gidan rediyon Kaduna. Wannan abu ya ba ni mamaki domin har Kaduna na je na tambayi wani dana da ke aiki gidan rediyon don jin wanda ya kai musu wakar daga nan Katsina kamar yadda na yi tsammani, amma sai ya shaida mini cewa Shatan ne ya yi ta a nan suka dauka. Wata rana Shata ya zo har gidana ya ce, in kirawo masa Alhaji Haruna Mashi inda yake cewa shin Haruna Mashi (marigayi) na ji an ce kana takara yaya baka shaida mini ba, don in yada ka? Gabana aka yi wannan, shi kuma Haruna Mashi ya ce masa zai aiko ni wajensa, ya kuma ba ni Naira dubu 50 na kai wa Shatan a can Funtuwa. Har ma lokacin da na je gidan ban same shi ba aka ce yana Dikke Sabon Layi can na kai masa sakon ya kuma ce in bari sai wanshekare na taho saboda mun je da dare. To wani abin da ya ba ni mamaki shi ne, kafin in kai ga tahowa, muna tare sai ga aiken mota an kawo masa kyauta daga Mustafa danraka, gogan sai kawai cewa ya yi a mayar masa ba ya karba. Da na so jin dalili sai ya ce, to, haka kawai zan hau motar babu mai? Kafin wani lokaci sai ga yaro ya dawo da motar da kudin mai Naira dubu 50.
Alaka ta kullu sosai tsakanina da Shata domin har akwai lokacin da ya zo gidana da daya daga cikin matansa amma daga bari in je nan in dawo sai da ta yi kwana uku ba Shata balle dalilinsa. Sannan sai ga direba ya turo ya dauke ta ya kai Funtuwa ya dauki ta Funtuwar ya kai masa ita Kano. Ashe fitar da ya yi Kano ya nufa. Hakika duk lokacin da Shata zai zo Katsina ba ya da wajen zuwa irin gidana. Kuma in ya zo ba abin da yake cewa a dafa masa sai kan rago kuma daga kwakwalwa sai idanu kawai yake ci.
Aminiya: Yaya kake kallon wakokin Shata?
Ado Kankiya: Shata! Shata!! Shata Ibilishi ne wanda Allah Ya ba basira. Dalilin da ya sa na ce Ibilishi ne Allah Ya ba shi basira shi ne, akwai wata rana muna tare da shi sai na tambaye shi cewa a cikin wakarsa akwai inda yake cewa, “An tara marokan birni, an tara marokan kauye.” sai ya ce na san wakar. Sai na ce, to yaya aka yi? Sai ya ce, an tara makada da maroka ne, bayan duk sun yi ’yan tsubbace-tsubbacensu ana cewa, ai mashiririci ne ba zai zo ba, sai gani na zo. Ya ce, duk mutumin da ke wajen sai dai ya ce ya ga shigar yaransa a cikin fili amma ba wanda ya ga shigarsa, dama an ce shi zai fara waka. To ya amshi amsa-kuwwa ya fara waka, sai Alhaji Ya’u Wazirinsa ya duko ya ce masa ba su jin abin da yake cewa. Budar bakinsa sai ya ce, sun yi mini sammu. Sai ya ce, a je a samo masa dashiya (sabuwar kwarya) a zubo ruwa a ciki aka masa. Da aka kawo masa sai ya gumtsi ruwan ya kurkure bakinsa ya kuma mayar da ruwan cikin kwaryar sai ga allurai uku. Ya sake yin haka bai zubo komai ba, ai sai waka ta tashi kowa na jin sa. To da na tambaye shi wanda ya ce ya yi wadannan abubuwa sai ya ce, ji ya yi kamar yana cikin mafarki ne aka ce ya yi haka.
Aminiya: Ko wakokin Shata sun yi tasiri ga harshen Hausa?
Ado Kankiya: Sosai! Ai wannan tasirin ya sa in ba a manta ba har wani shiri makada da mawaka suka taba yi na cewa, duk mai son ci gaba da waka to, sai ya yanki lasisi. Ba kuma komai ya kawo haka ba sai ganin irin yadda ya mamaye komai, tun a wancan lokacin amma kuma abin bai je ko’ina ba, kamar yadda shi ma bai shiga kungiyar da aka so har korarsa a yi a kuma hana shi wakar ba. Kuma ina iya tunawa akwai wani abin mamakin da na gani a wata rana da na je Funtuwa inda ya dauke ni muka je gidan da yake kiwon kadoji. Da muka shiga sai ya ce mini, yau zan gane mai cinye mini agwagwi da kaji. Zan kira su duk wanda ka ga ya tsaya daga baya, to shi ne. Ya kuma kira su kamar mutane sai ga wani kato ya tsaya daga baya. Sai ya yi masa tsawa cewa ya iso kusa da shi, ya kuma matso, sai ya ce masa daga wannan rana ya sake yi masa barna sai ya yanka shi. Ya ce su koma suka koma cikin ruwa.
Aminiya: To yanzu yaya kuke ganin wakokinsa?
Ado Kankiya: To gaskiya a yanzu dai babu kamarsa kuma ba a iya maimata kamarsa. Mafi yawan wakokin zamanin da ake sa wa masu saurarensu ba su san abin da masu wakar suke cewa ba balle fahimta. Amma ga Shata, ko wanda bai jin Hausa sosai sai ya gane me yake cewa a cikin wakar.
Aminiya: Ko akwai wani jan hankali da za ka yi?
Ado Kankiya: Kirana ga gidajen rediyo da talabijin ne na cewa su rika sanyo wokokinsa domin amfanar matasanmu na wannan lokacin da Hausa take neman barinsu ko suke gab ga barinta ta fuskar sauraren wakoki masu ma’ana. In da Shata ya kawo wannan lokacin ya ga irin yadda Najeriya ta koma da sai ya yi mamaki. Ina rokon Allah Ya sa mu gama lafiya.