✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na’ibin Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu

Sheikh Umar Suleman ya rasu ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya.

Sheikh Umar Suleman, wanda shi ne Nai’ibin  Babban Shehin Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu.

Shiekh Umar Suleman ya rasu a ranar Litinin yana da shekara 76 a gidansa bayan fama rashin lafiya.

Dansa, Khadi Mustapha ya ce, “Mahaifina, Shiekh Umar Suleman ya rasu yau (Litinin) da rana a gidansa da ke Unguwar Kanawa, Kaduna bayan fama da rashin lafiya. Ya rasu yana da shekara 76.

“Kafin rasuwarsa, shi ne Nai’ibin fitaccen malamin Islama, Shiekh Dahiru Usman Bauchi, malami ne kuma jagoran al’umma.”

Mustapha Suleman ya ce marigayin ya rasu ya bar ’ya’ya 17 children da jikoki da dama.

Ya kuma tabbatar mana cewa ya tuni aka fara shirye-shiryen jana’izarsa.