Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Nahiyar Afirka na da dukkanin abubuwan da ake buƙata domin ta iya dogara da kanta.
Ya ce Afirka na da arzikin ƙasa, mutane masu hazaƙa, da dukiyar da za ta iya amfani da su domin ciyar da nahiyar gaba.
Tinubu ya yi wannan bayani ne a Abu Dhabi, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, a ranar Litinin lokacin da ya gana da Shugaban Ƙasar Rwanda, Paul Kagame.
A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce:
“A yammacin yau, na yi ganawar faɗaɗa fahimta tare da Shugaban Ƙasar Rwanda, Paul Kagame.
“Nahiyar Afirka na da dukkanin albarkatun da ake buƙata domin ciyar da kanta gaba.
“Muna da ɗimbin arziki, mutane masu fasaha, da ƙwarewa. Abin da ya rage gare mu shi ne mu inganta haɗin kanmu da kasuwancin ƙasashen Afirka domin amfanin mutane da nahiyar baki ɗaya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa “Yanzu ne lokacin da Afirka za ta nuna ƙimarta a duniya.”
Tinubu ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kan ƙasashen Afirka wajen samun ci gaba mai ɗorewa.
Ya ce, “Dole ne mu daina dogaro da ƙasashen waje kuma mu fara amfani da arzikinmu don amfaninmu.
“Wannan shi ne matakin farko na samun cikakken ‘yancin tattalin arziƙi da ci gaba.”
Shugaban Rwandan, Paul Kagame, ya amince da ra’ayin Tinubu.
Ya bayyana cewar, “Afirka tana buƙatar shugabanni masu hangen nesa da ƙwazon yin aiki tare don magance matsalolin da suka shafi tattalin arziƙi, tsaro, da ilimi.”
Taron Abu Dhabi, ya bai wa shugabannin damar su tattauna hanyoyin haɗin kai tsakanin ƙasashen duniya da samar da tsare-tsaren da za su kawo ci gaba a sassa daban-daban, musamman a Afirka.
Har wa yau, masana sun jaddada cewa Afirka na da albarkatun ƙasa kamar ma’adinai, man fetur, da kuma filaye masu kyau don noma.
Sai dai sun ce rashin haɗin kai da rashin ingantattun tsare-tsare na daga cikin matsalolin da suka hana nahiyar cimma burinta.
Tinubu, ya ƙarfafa batun kafa hanyoyin kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka da ƙarfin masana’antu da fasaha a cikin gida, wanda zai rage dogaro da kayayyakin waje.
Ana fatan irin wannan tattaunawa tsakanin shugabannin Afirka za ta haifar da sauyi mai kyau ga nahiyar baki ɗaya.