Hukumar NAHCON mai kula da harkokin aikin Hajji a Najeriya, ta mika bukatar neman kafa Cibiyar Horo kan Aikin Hajji ta kasa ga Hukumar da ke kula da ingancin ilimin kimiya ta Tarayya (NBTE).
Shugaban NAHCON Zikrullah Kunle Hassan yayin gabatar da wasikar bukatar ga babban sakataren Hukumar NBTE, Mas’udu Adamu Kazaure, a Kaduna, ya ce bukatar assasa cibiyar ta zama wajibi domin tabbatar da aikin Hajji cikin tsari.
Ya ce NAHCON tana gogayya da sauran manyan ma’aikatu masu girma da ke bukatar mutane masu ilimin zamani da cikakken tsari na sanin abin da masana’antar ta kunsa a duk harkokin gudanarwa.
“Muna son horas da mutane da tattara bayanai tare da tantance su, horas da malamai da samar da kundin tsari da kafa ka’idodi ga maniyyata aikin Hajji.
“Muna son bayar da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya,” inji shi.
Alhaji Zikrullah ya kara da cewa, Hukumar tana da niyyar wallafa littafai da bayanai cikin rubutu da bidiyo na yadda alhazai za su rika gudanar aikin Hajji, domin inganta harkokin gudanarwa na cibiyar.