✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAHCON ta bayyana kamfanin jirgin da zai yi jigilar alhazan Kano

Rikicin Sudan zai kawo wa jigilar alhazai a bana cikas.

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ba wa Kamfanin Max Air aikin jigilar maniyyatan Jihar Kano su 5,917 zuwa Saudiyya domin sauke farali a Hajjin bana.

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Muhammad Abba Dambatta ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Talata.

Idan za’a iya tunawa Aminiya ta rawaito cewa matakin da NAHCON ta dauka na ba wa Kamfanin Azman Air jigilar maniyyatan jihar a shekarar da ta gabata ya fuskanci gagarumar suka daga Hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Kano da kuma gwamnatin jihar.

Kamfanin Max Air dai ya dade yana jigilar alhazan jihar har zuwa shekarar da ta gabata a lokacin da sabon Shugaban Hukumar NAHCON ya ba wa Kamfanin Azman Air aikin jigilar.

Ya kara da cewa jirgin yana da inganci kuma yana da jiragen sama guda uku masu daukar fasinja 1,000 , wanda hakan zai kawo saurin kwashe maniyyatan a bana.

Haka kuma, Muhammad Dambatta ya sanar da cewa hukumar ta rufe yin sabuwar rajistar aikin Hajjin sakamakon umarnin da NAHCON ta bayar.

A cewarsa, an samu kujeru kusan 6,000 da Hukumar NAHCON ta ware wa maniyyatan Kano.

Ya kara da cewa kawo yanzu, maniyyata 4,900 sun kammala biyan kudin Aikin Hajjin baki daya, yayin da sauran wadanda suka ajiye Naira miliyan 2.5 za su cika ragowar kudin nan da kwanaki masu zuwa.

Abba Dambatta ya kuma bayyana cewa hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da aikin Hajjin bana.

“Mun kammala dukkan shirye-shirye tun daga wurin kwana da ciyarwa da jigilar kaya daga Jeddah zuwa Makkah da Makkah zuwa Madina.

“Mun shirya don hawan jirgi. Mun yi tsari mai kyau wanda zai tabbatar da alhazan bana sun mori kudin da suka biya.

“Mahajjatanmu za su yi rayuwa mai kyau a Saudiyya,” Dambatta ya tabbatar.

Ya kuma ce akwai yiyuwar NAHCON ta rage lokacin tashin jigilar alhazan Najeriya sakamakon yakin da ake yi a kasar Sudan.

“Duba da cewa a yanzu sakamakon yakin da ake yi a Kasar Sudan ya janyo ake samun karin awanni wajen jigilar alhazai a maimakon awanni hudu.

“A yanzu ana yin awanni bakwai zuwa takwas don haka akwai yiyuwar Hukumar NAHCON ta matso da lokacin fara jigilar alhazai daga 21 ga watan Mayu zuwa yanzu kasa da haka.”