✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAFDAC za ta fara dirar mikiya kan masu maganin gargajiya a Kaduna

NAFDAC ta ce yadda ake tallata magungunan abin damuwa ne.

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta ce za ta fara kamen masu sayarwa da kuma tallata magungunan gargajiya ba bisa ka’ida ba a Jihar Kaduna.

Jami’in hukumar a Jihar, Nasiru Mato ne ya sanar da haka yayin wata zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Kaduna ranar Litinin.

Ya ce yadda masu tallan magungunan ke wuce gona da iri a Jihar abin damuwa ne matuka kuma ya zama wajibi a dauki mataki a kai.

“Magungunan gargajiya suna da matukar tarihi kuma tun farkon dan Adam ake amfani da su. Amma a ’yan shekarun nan, yadda ake tallata su ba bisa ka’ida ba abin damuwa ne matuka.

“NAFDAC na da alhakin kula da kuma tabbatar da yadda ake sarrafawa da shigowa da fitarwa da rarrabawa da tallatawa da kuma amfani da su.

“A sakamakon haka, dole wadannan magungunan su bi dukkan ka’idojin gwaje-gwaje domin tabbatar da ingancinsu da kuma tabbatar da an yi musu rijista kafin a fara amfani da su,” inji shi.

Daga nan sai jami’in ya shawarci masu tallan magungunan gargajiyar da su amsa bukatar hukumar wajen ganin sun yi rijista tare da samun takardun izinin sarrafa su domin kaucewa fishin hukumar.

“NAFDAC a shirye take ta inganta yadda ake hada-hadar magungunan na gargajiya domin su daidaita da tsarin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma,” inji Nasiru Mato.

Ya kuma jaddada aniyar hukumar wajen tabbatar da bin ka’ida da kuma wayar da kan jama’a don ganin an magance matsalar masu sayar da jabun magungunan a Jihar.

Sai dai ya ce hukumar za ta yi dirar mikiya a kan duk wanda yake yin sana’ar ba bisa ka’ida ba domin kare rayukan al’umma.