✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NAFDAC ta lalata ‘Tramadol’ ta Naira tiriliyan 1.7

Kashi 70 na magungunan da ake amfani da su a Najeriya daga ketare ake shigowa da su.

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NAFDAC), ta ce ta lalata kwayoyin Tramadol na sama da Naira tiriliyan N1.7 da ta kama a tsakanin shekaru biyar.

Shugaban Hukumar, Farfesa Moji Adeyeye ce ta bayyana haka a wajen wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata.

Ta ce kafin 2018, kasar nan na fama da kwararar kwayar Tramadol wanda ke barazana ga lafiyar al’ummar kasa, musamman matasa.

Ta kara da cewa, a baya-bayan nan sun kama tare da lalata haramtattun magunguna na kimanin biliyan N1.3 a fadin kasa.

Adeyeye ta nuna damuwarta kan yadda ake samun karuwar kamfanonin sarrafa magunguna a China da Indiya wadanda ba su aiwatar da gwaje-gwajen tantance inganci magungunansu kafin tura wa kasashe, hasali ma ba su da kayan aikin gwajin.

Ta nuna damuwar ce duba da kashi 70 cikin 100 na magungunan da ake amfani da su a Najeriya daga ketare ake shigowa da su.

Ta ce, “Wanan ya sa muka rattaba hannu a yarjejeniya da dakunan bincike da jami’an CIR, wanda a dalilin haka mun dakatar da sama da 85 zuwa 90 na shigo da magunguna.”

%d bloggers like this: