✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Na yi wa matar aure fyade a kullum na tsawon watanni biyar’

Na turke ta a wani daki na tsawon watanni biyar inda a kullum na ke yi mata fyade.

Wani kasurgumin dan daban daji mai suna Surajo Dauda, ya shiga hannun rundunar ’yan sanda a Jihar Katsina.

A cewar Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa, dan daban dajin mai shekaru 30 na daga cikin mutanen da rundunar ta yi holensu kan zargin aikata miyagun laifuka.

Ya ce Dauda wanda mutumin Kauyen Rijiyar Basai ne da ke Karamar Hukumar Danja a Jihar Katsina, ya bayyana yadda ya rika yi wa wata matar aure daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da su fyade.

SP Gambo ya ce matar mai suna Jamila Auwal mai shekaru 18, an sace ta ne a Kauyen Tandama bayan an gusar mata da hankali.

Ya ce Dauda ya furta cewar bayan sace ta, ya kuma turke ta a wani daki na tsawon watanni biyar inda a kullum ya ke yi mata fyade.

Kazalika, Kakakin ’yan sanda ya ce sun samu nasarar cafke wani dan daban daji mai suna Ibrahim Iliya, wanda mutumin Kauyen Sabon Garin Dan Ali ne da ke Karamar Hukumar Danmusa ta Jihar.

“A yayin binciken da muka gudanar, wanda ake zargin ya bayyana mana cewa yana daga cikin gungun ’yan bindigar da suka kai hari gidan gonar wani Alhaji Abubakar a Kauyen Yantumaki da ke Karamar Hukumar Danmusa a ranar 1 ga watan Afrilun 2021.

“Ya ce sun yi awon gaba da Shanu 49, Tumaki 41 da Awaki 13 wanda darajarsu ta haura Naira miliyan biyar,” a cewar SP Gambo.

Bayanai sun ce wanda ake zargin ya amsa cewa shi da wasu mutum 17 ne suka kai harin wanda a yanzu an bazama wajen taso keyarsu.