Matashin nan da aka kama kan yi wa wani ɗan shekara 28 yankan rago a garin Damaturu, Jihar Yobe, ya ce ya yi haka ne don kada ya biya bashin N500,000 da marigayin yake bin sa.
Wanda ake zargin, mai shekaru 24, ya bayyana cewa ya kashe Marigayi Lawan Adamu, wanda maigidansa ne saboda tunanin hakan zai ba shi damar cinye kuɗaɗen ba tare da kowa ya sani ba.
A kwanakin baya ’yan sanda suka kama shi bisa zargin kashe Lawan Adamu ɗan a unguwar Nayi-Nawa cikin garin Damaturu kan zargin kisa ta hanyar yankan rago.
Wanda ake zargin ya bayyana cewa, ya karbi bashin N500,000 a ƙarƙashin tsarin raba riba daga Marigayi Lawan Adamu ne a shekarar 2023 da ta gabata.
Ya ƙara da cewar, marigayin ya nemi ya biya shi kuɗinsa ne saboda ya saɓa ƙa’idar da suka yi da shi na bayar da riba.
Shi kuma, ba ya son biyan marigayin kudin nasa, don haka, sai ya yanke shawarar hallaka shi, kuma ya aikata hakan.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim, wanda ya tabbatar da kisan, ya ce wanda ake zargin ya shaida wa Sashen Binciken Ƙwaƙwaf na laifuka (CID) cewa ya kashe Lawan Adamu ne saboda ba zai iya biyan N500,000 da ya ba shi rance don gudanar da harkokin kasuwancinsa ba.
DSP Dungus ya ƙara da cewar, da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da shi a gaban ƙuliya don fuskantar hukuncin da ya dace da abin da ya aikata domin ya zama izina ga masu irin wannan mummunan ƙudiri.