✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yi nadamar shirya wasannin dambe – Alhaji Muhammadu dan Dambe

Sardauna Ahmadu Bello ne  ya kawo Alhaji Muhammadu Mai-Nama dan Dambe Unguwar Sarki da ke Kaduna bayan da ya buge wani dan Nijar a kokuwa.…

Sardauna Ahmadu Bello ne  ya kawo Alhaji Muhammadu Mai-Nama dan Dambe Unguwar Sarki da ke Kaduna bayan da ya buge wani dan Nijar a kokuwa. Ya yi suna ne dangane da harhar fawa da kuma shirya wasan dambe kafin ya tuba. Ko mene ne dalili?
Menene tarihin ka?
 Suna na Alhaji Muhammad Mai-Nama dan-Danbe Unguwar Sarki Kaduna. Ni mutumin Galadanci ne na Gwadabawan Sakkwato. Kuma sana’ar fawa na gada a gidanmu. Yanzu shekaruna a Kaduna 53.
 Ya aka yi ka samu sunan dan dambe?
 kanin mahaifina Abubakar Garba ya yi gangamin ’yan dambe ran sunana a kofar gidanmu. Dililin wannan suna ke nan.
 Mene ne dalilin zuwan ka garin Kaduna?
 Ranar da aka bude gidan Sardauna da ke Sakkwato muka yi wasan kokuwa. Wani dan kokuwa yana taka kafa guda-guda ana yi masa kida. Da muka raba turmi, Allah Ya ba ni sa’a na kada shi, Sardauna ya ji dadi.
 Da za a bude gidan Sarkin Musulmi da ke Kaduna inda aka binne Sardauna, sai aka aika Sarkin Samari Mailafiya na Sakkwato har Yamai na birnin Nijar ya je ja taho da ni. Sannan da yamma muna zuwa gidan Sardauna mu yi gaisuwa. Ni da Sarkin Fawa Sa’adu yana Unguwar Shanu.
 Sannan aka yi biki a bakin titin-dogon Unguwan Shanu na zuwan Saruaniya da na NPC, jam’iyyar Sardauna. Daga nan na je gida, na shirya, na dawo Kaduna.  Ina da ‘ya’ya 21 masu rai da jikoki 73. Sannan ba ko yaushe ake wasan kokuwa ba, kuma in an je tarom siyasa, sai mu daga tuta.
 Yaya aka yi ka fara harkar dambe?
 Yadda na zama Oganiza na dambe ya faro ne a unguwar Kawo, Kaduna a wani Otal, sannan na dawo da shi gefen gidan jaridar New Nigerian, NNN, in da aka gina hawa 15 na ginin Nagwamatse, anan muka yi wasan ‘Daba 77’ da na ‘Taban Taget’.
 Anan aka yi abin mamaki inda Kai-Kadai-Gayya ya yi kwanton bauna zai kaiwa Shago duka a bayan sun bar dambe da dadewa, Sai dan Anache ya ce kai. Sai Shago ya waiga ya ganshi ya mike, amma aka raba. dan-Anache ya so ne ya hada rigima. Sai Shago, dan Dunawa da Kai-Kadai-Gayya suka fito daya bayan daya suka yi kirari. Sannan dan Anache ya yi musu waka. Amma da Kai-Kadai-Gayya ya kai dukan da ba kyau.
 Yaya aka yi ka saba da Shago da sauran su?
 In sun zo garin nan suka gaishe da Sardauna sai sun zo sun same ni. Har lokacin da suka bar zuwa nan garin. Ni ne mai masaukin su. Duk sun rasu ni kadai na rage, kafin na tuba. Shago mutumin Yarkohogi ta Zamfara ne. dandunawa kuma Ba-Dauri ne, shi kuma Kai-Kadai-Gayya Bakatsine ne mutumin Danja. Sai dai dandunawa ya fi su girman jiki. Shago sadauki ne kuma yana da mawaki. dandunawa sun buga da Shago a gidan Zana, Sakkwato. Sannan kuma a Gusau. Sai wata yarinya ta ce ‘laa Shago ya fadi’ amma nan take ta mutu. dan dunawa kanshi bai ga faduwar ba. Kai-Kadai-Gayya sun taba bugawa da shago a Funtuwa.
 Kudi suka sa ake yin dambe ko neman suna?
 Neman suna kawai ake nema.  Don a kudu akwai mutum dari 4 a Arewa akwai mutum dari 5, Arewa sun fi yawa. Duk ni ke dawainiyar abinci da  hidima da  sutura da magani da dai sauransu. Kudin tikiti da ake karba ba su ta-ka-karya-balle-su-karya ba. Mutanen kudu sune Kanawa da Katsinawa sun hada da Kai-Kadai-Gayya da dan Dunawa da Kure da Ado- dan-Kure da Anene da Tushiya da dai sauransu. Sannan Arewa sun hada da Sakkwato da Zamfara.  Su ne Shago da Ada-Na-Jan-Ruwa da Sanin-Basafce. Sannan dan-Dunawa da Kai-Kadai-Gayya ba su taba bugawa ba.
 Me ya sa in Shago ya karbi karin kudi sai ya ba dan Anace?
 Shago na mika hula in ya yi kisa don a yi masa kari, sai ya juye wa dan-Anache. Amma ban san ko in an koma gida suna wata dabara ce su raba ba. Shi dan-Dunawa yana da irin nasu makada na Kudu, Kanawa.
 Hayar fili kuke kamawa da ’yan sanda ko ko?
 Ni na ke kama hayan fili in na je na karbi fam sai in kaiwa marigayi Alhaji Umaru Dikko yana Kwamishinan Al’adu ya sa hannu shi ke nan. Da Alhaji Sa’adu Shugaban karamar hukuma. Ba su taba cewa in ba su ko kwabo ba. Suna zuwa wajen kallon wasan bayan la’asar.
 Akwai riba kuwa?
 Nishadi ya fi yawa. Don na fi sa karfin aljihu a wasan.
 Me ya sa ka bar harkar Dambe?
 Na Tuba. Dalili kuwa shi ne na yi tambaya ce inda Malamai suka ce akwai zunubi don ana haduwa ne maza da mata. Don wata za ta san gidan wani, wani ya san gidan wata. Shi ya sa na tuba. Tun daga lokacin ban sake halartar filin wasan dambe ba yau kimanin shekaru 30 ke nan. Kuma na lalata hotuna da duk wani abu na dambe.  Amma dan uwana, Alhaji Muhammadu Mai Nama Gada-Gada Unguwar Shanu ya taba shiryawa shi ma ya bari. ‘Yan Tudun Wada suka fara suka bari.
 Ya maganar asiri a tsakanin ’yan dambe?
 Wasu na zuwa da Malamansu, wasu su kauce, don kar su fadi. Wani da guraye, da layu da karafuna, wani kuwa sai ya shigo fili zai tube.
 Yaya aka yi a tsakanin dan-Fashi mai suna ‘Doki- dan-Ali’ da Audu-Kai-Kadai Gayya?
 An ce Tsohon barawo Doki Dan Ali idan ya yi sata sai ya tsaya yana kirari a Unguwan Shanu cewa in da namiji ya fito. Sai Kai-Kadai- Gayya ya zo ya yi masa bugu daya, ya fadi kwace ya sume har sai da hantsi sannan ya tashi.
 Ko kana da Sarauta?
An ce za a ba ni sarkin pawa sai na ce a ba yara. Aka ba Ahmadu. Sai dai an ba ni  mukamin kula da Masallacin Sultan Bello na shekaru 28. Daga baya aka ban takarda an sauke ni an ba yarona. Sannan a sana’ar fawa na gode Allah don wasu sun bar garin, sun gudu.  In ka ga ban yi yanka ba to na yi kwantan nama ne.
 Shin kana siyasa?
 Tun rasuwar Sardaun na bari. Ba ruwana.