✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yi mamakin shigar ASUU yajin aiki —Ministan Ilimi

Ba zan iya cewa ga lokacin da za mu warware matalsar ba.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya ce abin mamaki ne hukuncin da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU ta dauka na tafiya yajin aiki na tsawon wata guda.

Kalaman Ministan na zuwa ne yayin ganawa da manema labarai a Fadar Gwamnatin Najeriya bayan kammala Taron Majalisar Zartaswa wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta ranar Laraba a Abuja.

Malam Adamu ya ce kada a zargi Gwamnatin Tarayya idan har ba a cimma maslaha ba a takaddamar da ke tsakaninta da kungiyar ASUU, yana mai cewa yajin aikin na ba zata da malaman jami’o’in suka tsunduma na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa a teburin sulhu tsakanin bangarorin biyu.

A cewarsa: “Abun takaici ne yadda ASUU ta tsunduma yajin aiki a daidai wannan lokaci, don yanzu neman su muke saboda a warware duk wata tankiya da ke tsakaninta da Gwamnatin Tarayya.

“Abu na karshe da ya wakana shi ne kwamitinmu ya duba bukatunsu amma ana ci gaba da tattaunawa a kansu.

“Sun gabatar da duk wata bukata wadda Ma’aikatar Ilimi ke ci gaba da nazari a kai.

“Yanzu haka akwai kwamitin da yake dubawa. Idan ya kammala, gwamnati a shirye take ta sanar da abin da za ta iya amincewa da shi, sai kwatsam na ji sun tafi yajin aiki.”

Dangane da zargin da ASUU ta yi kan rashin halartar ministan zaman tattaunawa da ita, ya ce: “ASUU ba za ta taba fadin haka ba. Kullum nakan kira taron da kaina. Tarukan da ban halarta ba su ne wadanda suka gudana a lokacin da na je ganin likita a Jamus.

“Muna son a cimma matsaya cikin lumana. Gwamnatin Tarayya a shirye ta ke ta gana da su a kan dukkan batutuwan da suka tattauna sannan idan aka ci gaba da yin zama da yawa kuma ba a samu an cike gibin ba, to ina ganin laifin ba na gwamnati ba ne.

“Akwai mafita kan wannan. Tattaunawar ita ce mafita, shi ya sa na ce na yi mamaki da ASUU ta shiga yajin aiki.

Da yake magana kan lokacin da za a cimma matsaya, Ministan ya kara da cewa: “Ba zan iya cewa ga lokaci ba. A shirye nake na cimma matsaya da ASUU a yanzu, amma tun da ba ni kadai ba ne, ba zan iya cewa ga lokacin da za a warware matsalar ba amma ina mai tabbatar da cewa za mu cimma matsaya nan ba da jimawa ba.”

Aminiya ta ruwaito cewa, a safiyar Litinin da ta gabata ce Kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki na wata guda domin jan kunnen Gwamnatin Tarayya wajen ganin ta cimma yarjejeniyar da suka kulla tsawon shekaru.

Har wa yau, daga cikin manyan muradan da kungiyar ta ke hankoro akwai neman amincewar gwamnatin a kan tsarin biyan albashin ma’aikatan jami’a da ake kira UTAS sabanin wanda gwamnatin ta bijiro da shi na albashin bai daya da ake yi wa lakabi da IPPIS.

Akwai kuma kuma bukatar neman matsaw a gwamnati ta samar da kayyyakin aiki a jami’o’i domin bai wa dalibai damar koyo da kuma gogayya da takwarorinsu na ko ina a duniya.