✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na shafe wata daya ban ga Tinubu ba — Wanda ya je Legas a keke

Sai dai ya ce duk da rashin ganin Tinubu, ba ya da-na-sani

Gaddafi Musa matashi dan asalin Jihar Katsina da ya tuka keke daga garin Funtuwa zuwa Legas domin murnar nasarar da zababben Shugaban kasa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya samu, ya bayyana wa Aminiya yadda tafiyar tasa ta kasance da irin kalubalen da ya fuskanta tare da yadda ya kasa cim ma burinsa na ganin Tinubu, lamarin da ya sa ya koma gida bayan ya shafe sama da wata guda bai gan shi ba:

Mene ne takaitaccen tarihinka da dalilin zuwa Leags a keke saboda nasarar Tinubu?

Sunana Gaddafi Musa, shekarata 26. Na kammala karatuna a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya. Na kudiri aniyar yi wa zababben Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tattaki, sai na zabi in tuko keke daga Funtuwa zuwa Legas don taya shi murnar nasarar da ya samu a zaben 2023, kuma na cika alkawarin da na yi duk da kalubalen da na fuskanta.

Ba ka samu turjiya ba lokaci da ka kudiri aniyar zuwa Legas daga Katsina a keke?

Na samu turjiya sosai domin mutum hudu kawai suka ba ni kwarin gwiwa, wato mahaifina da mahaifiyata sai abokaina biyu, amma mutane da dama sun yi ta yi min ba’a, suna yi min muguwar fata, inda suka ce ’yan bindiga za su sace ni a lokacin da nake tafiyar. Amma na gode wa Allah, na isa Legas lafiya bayan tafiyar kwana 14, duk da ban taba zuwa Legas ba, sai dai na taba zuwa garin Ogere a Jihar Ogun wanda yake kan hanyar Legas daga Ibadan.

Yaya tafiyar ta kasance?

Na fara tafiya ranar 26 ga Fabrairu bayan na kada kuri’ata ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben ranar 25 ga Fabrairu, inda na fara wannan tafiya da safe ba tare da jiran bayyana sakamakon zaben ba, da yake ina da yakinin Tinubu ne zai ci zaben. Na isa Zariya a Jihar Kaduna da yamma, inda na kwana na ci gaba da tafiya da safe. Na isa garin Rijana a Jihar Kaduna na kwana biyu a can.

Na hadu da wasu ’ya’yan Jam’iyyar APC a garin Suleja a Jihar Neja, lokacin da aka bayyana cewa Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ne ya lashe zaben, wanda hakan ya kara min kwarin gwiwa daga nan na ci gaba da tafiya zuwa garin Minna da Bidda da Mokwa, bayan na bar garin Mokwa da ke Jihar Neja wanda ba ya da nisa da garin da na fuskanci babban kalubale.

A garin mutane da dama sun taru suna maraba da ni, suna murna da ban-kwana da ni. A yayin da na bar su, wasu samari a kan babur sun bi ni zuwa wajen garin, suna tambaya ta ko ni wane ne? Ina zan je? Da na fada musu manufata, sai suka zage ni, suka ce min wawa, wai ina bata lokacina da kuzarina a kan wanda bai ma san da ni ba, sun so in biye masu mu yi fada, amma na ki, ban ce masu uffan ba. Ina da wayoyi uku a tare da ni, daya daga cikinsu na cikin aljihun gaba, nan suka sa hannu suka zare ta, ban yi musu gardama ba na ci gaba da tafiyata.

Wannan shi ne babban kalubalen da na fuskanta. Sai kuma wani kalubalen ta fuskar karancin takardun kudi, domin a lokacin da na fara wannan tafiya sai da na tabbatar ina da isassun takardun kudi a hannuna da kuma wasu a asusuna na banki. Niyyata ita ce in rika kwana a gidan Dagaci ko Mai Unguwa ko mai gari, a duk inda na yada zango, amma daga karshe hakan ya ci tura, domin da zarar na sauka a gari na nemi wani basarake sai ya ce ba zai sauke ni ba domin tafiyata ta ’yan siyasa ce.

Wasu suna hada ni da ’yan siyasa, amma sau tari ni nake biyan kudin otel da nake kwana, hakan ya sa kudin hannuna suka kare cikin kankanin lokaci, kuma hakan ya sa na gamu da babban kalubale domin idan na je zan ci abinci masu sayar da abincin kan hanya ba su karbar taransifa wanda haka ya tilasta ni zuwa saye a manyan kantuna wadanda na yi ta saya da tsada. Haka tayar kekena ta yi faci ba sau daya ba ba sau biyu ba, lokacin da na yi faci da yawa naka sauya tib din tayar kuma ina bukatar kudi don yin haka.

Akwai wata mata a Mokwa a Jihar Neja, ’yar kabilar Ibo wadda take sayar da kekuna, lokacin da na yi faci ina shiga shagonta, da ta gan ni sai ta yi ta murna ta ce ta karanta labarina a Soshiyal Midiya, inda ta ba da kudi aka sayo tib kuma ta biya mai gyara don ya sa min tib din a keke.

Na yi farin cikin haduwa da ita, kuma kafin haduwa da ita a wannan yanki na Jihar Neja lokacin da na yi faci na je na sayi tib din a hannun wani mutum, wanda shi kuma ya kara min farashi don kawai ya fahimci cewa ina tuka keken ne saboda Asiwaju, amma ba ni da wani zabi illa in saya haka.

Kuma abin da ya ba ni mamaki shi ne lokacin da na isa jihar Oyo, nan ma na yi faci, sai na hadu da wani mai faci a gefen hanya. Bayan ya yi min faci, sai ya ce in ba shi Naira 500, na ce masa Naira 50 nake biya idan an yi min faci a Arewa. Sai ya ce ai Jihar Oyo ba Arewa ba ce, kuma ba ni da wani zabi face in biya shi 500 a faci daya kacal, haka kuma aka yi sai da na biya. Wannan abu ya ba ni mamaki.

Ko mutane sun tare ka lokacin da kake tafiya?

Eh, mutane sun yi ta tare ni, suna daukar hoto da ni, kuma a lokacin da na isa Ibadan ’yan jarida da dama ne suka tare ne, domin na riga na zanta da wasu ’yan jarida a garin Oyo wadanda suka watsa labarin zuwana a gidan rediyo. Don haka a duk lokacin da na wuce manyan hanyoyi mutane suna jinjina min, domin sun ji sanarwar zuwana a gidan rediyo.

A lokacin da na isa Ibadan ’yan jarida daga NTA da sauransu sun yi jiran zuwana, kuma na yi hira da su, mutane da yawa sun yi murna da ganina, suna daukar hotuna tare da ni, wani lokacin sai na yi da gaske sannan su kyale ni in tafi. Ina gaya musu cewa tafiyata na da nisa. Na kuma shiga Legas ranar Lahadi 14 ga Maris.

Me ya biyo bayan isarka Legas?

Duk da cewa na shafe kwana 16 a Legas ba tare da ganin Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ba, bayan duk kokarin da na yi ya ci tura, har yanzu ban yi nadamar tafiyar ba, kuma har yanzu ina da yakinin zan gana da Tinubu.

Burina shi ne in hadu da shi, idan na gan shi zan ba shi kyautar keken da na yi amfani da shi wajen tafiyar, kuma in ce masa ya dubi lamarin da ya shafi matasan Najeriya. Domin na yi wannan tafiya ce saboda matasan Najeriya da kuma jihata Katsina. Saboda ina so ya samar da dama ga matasan kasar nan don su samu ayyukan yi da kuma dogaro da kai.

Na kammala karatun NCE a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya, amma ba ni da aikin yi. Yawancin matasan Najeriya suna cikin irin wannan hali, kuma jihata Katsina ta sha fama da matsalar rashin tsaro a dalilin ayyukan ’yan bindiga. Ina so ya dubi wannan, ya yi la’akari da shi, shi ya sa nake son ganin sa. Haka kuma a yunkurina na karshe domin in gan shi a ranar zaben 18 ga Maris, wasu ’yan iska a yankin Fela Shrine sun tare ni, sun yi min fashi. Na je rumfar zaben Tinubu da ke Ikeja a ranar zaben domin in samu ganinsa a lokacin da ya zo kada kuri’a, amma ban samu haduwa da shi ba. Hatta ’yan jarida ba a yarda su yi magana da shi ba.

A hanyata ta komawa dakina na otel a kan kekena, wasu ’yan iskan gari suka afka min a yankin Fela Shrine, inda suka karbe min waya da jakata. Bayan na samu labarin Tinubu ya fita kasar waje lura da gararin da na shiga a Legas, sai na yanke shawarar na koma gida Katsina domin in karasa azumin da na soma a Legas. Bayan na isa can zuwa gaba zan ci gaba da yunkurin ganin Bola Tinubu domin ban fid da rai za mu hadu ba.

Yaya ka yi da keken naka, a kansa ka koma gida Katsina?

A jirgin sama na koma, kuma ka san ba zan iya hawa jirgin sama tare da keken ba. Saboda akwai lokacin da na hadu da Fola Tinubu, Darakta Janar na yakin neman zaben Tinubu. Bayan na hadu da shi a ranar Laraba 22 ga Maris kuma ya yi min kyakyawar tarba tare da jama’arsa, na ba da keke nawa domin ya isar da shi ga Tinubu, kuma ya yi min alkawarin zai kai masa. A ranar Lahadin makon jiya ne na hau jirgin sama zuwa Kano daga Kano na karasa Funtuwa.