✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na rasa mijin da babu kamarsa —Matar Sheikh Albani Kuri

Amaryar Sheikh Ibrahim Musa Albani Kuri ya siffanta wa Aminiya yadda ɓarayin waya suka yi masa kisan gilla a gabanta

Labarin kisan gillar da aka yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Gombe Shiekh Ibrahim Halliru Musa, (Albanin Kuri) ya girgiza al’ummar.

Sheikh Ibrahim Albanin Kuri, ya gamu da ajalinsa ne ta hanyar kisan gilla da ɓarayin waya suka masa a gidansa da ke unguwar Tabra a yankin Gona da ke Karamar Hukumar Akko a Jihar.

Bayan an wayi gari da kisan na sa Aminiya ta ziyarci iyalan mamacin inda ta samu zantawa da karamar matarsa da ya aura wata takwas da suka gabatar, wadda suke tare a lokacin da aka kashe shi, Fatima Muhammad.

Yadda aka yi wa Sheikh Albani Kuri kisan gilla a gaban amaryarsa

Cikin hawaye, Malama Fatima ta ce suna kwance kawai sai ɓarayin suka shiga musu gida sai ji kawai ta yi an gaura mata mari, ta tashi tana salati.

A nan ne shi ma mijin na ta ya tashi, sai suka ga mutum uku, ɗauke da wukake da bindiga a kansu kuma fuskokinsu a rufe.

Fatima, tace mutum biyu a cikin ɓarayin suka ce malam ya ba su waya, sai ya cire wayar a jikin power bank ya ba su, suka hada da power bank din suka dauka.

Suka je falo suka dauki nata suka sake dawowa suka nemi ya ba su kuɗi sai ya ce shi ba ya zuwa gida da kudi amma ga katin ATM dinsa, suka karba.

Tace a lokacin da suka karbi ATM din ne ya yi kokarin bude fuskar ɗayansu sai suka juyo suka caka masa wuka a ƙirji suka sare shi a hannun, suka buga mishi taɓarya a kafa suka karya shi.

A cewarta, watansu takwas da aure kuma tana son mijinta,  wanda ba ta jin cewa za ta sake samun kamarsa.

Allah Ya tona asirinsu —Mahaifiyarsa

Ita ma mahaifiyarsa, Malama Binta Halliru mai kimanin shekaru saba’in ta bayyana jimaminta bisa yadda ta rasa dan nata da yake kula da ita da sauran ’yan uwansa.

Ta ce tun da ta ji shigar ɓarayin gidan take tambaya ko Ibrahim ne, ta yi kira har sau biyu ba a amsa mata bam can sai ta ji ihun matar marigayin.

Nan take hankalinta ya tashi ta fito ta ga ashe ɓarayi ne, tun daga nan har gari ya waye ba ta iya sake yin barci ba, ba ta sani ba, ashe lokacin sun riga sun kashe shi ne.

Malama Binta, ta yi addu’ar Allah Ya jikan Malam Ibrahim, Ya sa yasa karshen wahalarsa ke nan, su kuma ɓarayin Allah Ya tona asirinsu.

Sheikh Ibrahim Halliru Musa Albanin Kuri ya rasu ya bar matan aure biyu da ’ya’ya bakwai.

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidan washegarin rasuwar, ɗaya matarsa tana hanyar zuwa daga garin Biu inda a can suke zama da marigayin a gidansa da ke can.

Kakakin rundunar ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya shaida wa wakilinmu cewa sun Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Oqua Etim ya hori Baturen ’yan Sandan yankin da ya gudanar da binciken don tabbatar da an kama wadanda suka aikata lamarin.

Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya, ya yi alkawarin kamuwa da hukunta waɗanda suka yi wannan aika aikan.