Manjo Hamza Al Mustapha, Babban Dogarin tsohon shugaban kasa na mulkin soja a Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha, ya ce ya yanke shawarar shiga harkokin siyasa a shekarar 2019 ne da niyyar samar wa matasan kasar damar cimma muradunsu na rayuwa.
Al-Mustapha ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), ya nemi tallafi daga kasashen Jamus da China game takarar tasa a zaben da ya wuce.
- Taho-mu-gamar jirgin kasa ta kashe mutum 40 a Pakistan
- Ku fito ku soki yunkurin kafa Biafra —’Yan Arewa ga manyan Ibo
“Na kafa jam’iyyar Green Party domin matasa da mata da talakawa da ma masu lalurar nakasa; jam’iyya ce da ke hankoron kyautata makomar Najeriya.
“Lura da rikice-rikicen da ke faruwa daga Kudanci zuwa Arewaci da kuma haduwata da mutanen da riginginmun suka shafa amma aka yi watsi da su; sai na yanke shawarar kafa jam’iyyar siyasar da za ta samar wa matasan Najeriya tudun dafawa wajen cimma burace-buracensu,” inji shi.
Al-Mustapha ya ce manufar ita ce karfafa matasan Najeriya ta hanyar samun kwarewa domin zama masu dogaro da kansu.
“Na tuntubi Jam’iyyar Green Party a Jamus da zimmar samun tallafin kudade domin koya wa matasanmu sana’o’i.
“Sannan na tuntubi daidaikun mutane a Koriya da China a kan ita wannan manufar tallafa wa matasan.
“Wadannan ababuwan ne daga karshe suka haifar da kafa jam’iyyar,’’ inji shi.
Sai dai Al-Mustapha ya ce saboda wasu dalilai bai iya yin takarar shugabancin kasa ba a zaben na 2019.
Ya ce tun da ita ma Jam’iyyarsa ta Green Party na daga cikin jam’iyyun da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soke rajistarsu, yanzu lallai ne ya nemi shiga inuwar wata jam’iyyar.
“In kana son jin cikakken bayani daga gare ni, to ka saurara sai karshen shekarar 2021, sannan ne za ka gan mu baro-baro,” inji shi.