✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗan sa-kai ya kashe matasa biyu a Borno

Majiyar ta ce wanda ake zargin Modu Mallam Gana ya harzuka da tsayarwar matasan a bakin ofishinsu, lamarin da ya bude musu wuta.

An kama wani jami’in rundunar sa-kai ta JTF, Modu Mallam Gana mai shekaru 27 a garin Monguno, bisa zarginsa da harbin wasu gungun matasa wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da raunata daya.

Wata majiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:15 na safiyar ranar 21 ga Maris, 2025, a lokacin da wasu matasa suka tsaya a gaban ofishin dakarun da ke Unguwar Bakin Kasuwa, a Karamar Hukumar Monguno.

Majiyar ta ce wanda ake zargin Modu Mallam Gana ya harzuka da tsayarwar matasan a bakin ofishinsu, lamarin da ya bude musu wuta.

Wadanda abin ya shafa — Ya’zainab Bum da Goni Mohammed Ahmadu — sun mutu nan take yayin da Hamsatu Ali ta samu munanan raunuka kuma aka kwantar da ita a babban asibitin Monguno.

Sai dai an tabbatar da mutuwar Ya’zainab Bum da Goni Mohammed Ahmadu, inda aka mika wa iyalansu gawarwakinsu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada yayin da Hamsatu Ali tana kwance a asibiti tana jinya.

Majiyar ta ce an kama wanda ake zargin nan take, kuma aka mika shi ga ‘yan sanda don gudanar da binciken da ya dace da shi.