Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wanda aka tube daga gadon sarauta ranar Litinin, ya yi jawabi ga ‘yan jihar inda ya gode musu bisa hadin kan da suka ba shi lokacin da yake kan gadon sarauta.
Sarki Sanusi II ya yi jawabin na minti 4 da dakika 40 ne kafin a fitar da shi zuwa jihar Nasarawa.
Ga yadda jawabin yake:
Bismillahir Rahmanir-rahim. Alhamdulillah. Wassalatu wassalamu ala rasulillah. Sayyadina wanabiyina Muhammadun Ibn Abdullah. Wa’ala alihi wasahbihi waman wa’ala.
Jama’a, as salamu alaikum wabarakatuhu.
A kullum muna cikin godiya ga Allah Subhanahu wata’ala a cikin ni’imominsa wadanda ba sa karewa.
Cikin ni’imomin da Allah Ya yi min, Allah Subhanahu wata’ala Ya kaddara an nada ni Sarkin Kano ranar takwas ga watan June shekara ta 2014. Ya raya ni a cikin rayuwa da lafiya. Shekara kusan shida a kan wannan gado da wannan gado namu mai albarka.
A yau Ubangiji subhanahu wata’ala wanda Ya ba da sarauta Ya kaddara Ya karba.
Ko da yaushe muna fada, cewa sarauta ajali ne da ita; kwanakin da Allah Ya rubuta a kan gado kayyadaddu ne. Idan ranakun nan sun zo, ko ana so ko ba a so sai an tafi. Saboda haka mu mun karbi dukkanin abin da Allah Ya yi. Mun yarda, mun gode, mun yi farin ciki. Kuma mun san shi ne alheri a gare mu. Muna gode wa al’umma a dukkanin shekarun nan— kauna da suka nuna mana, da soyayya da biyayya da addu’o’i.
Muna gode wa dukkanin wadanda suka taimaka mana a cikin harkar mulki— ‘yan majalisarmu da hakimai— da suka ba mu goyon baya.
Muna gode wa ‘yan uwa na zumunci wadanda suka tsaya suka kare martabarmu da martabar gidan nan. Muna kira ga al’umma a zauna lafiya. Wanda Allah Ya ba wa sarauta, mun umarci iyalanmu da ‘ya’yanmu da wadanda muke da iko a kansu, duk wanda Allah Ya ba wa, al’umma suka yi mubaya’a, su je su yi masa mubaya’a. Su bi shi, su kare martabarsa, su kare mutuncinsa. Saboda martabarsa da mutuncinsa ita ce martabar wannan gida.
Muna gode wa ‘yan uwa, muna hakuruntar da su, muna tabbatar musu cewa, Allah ba Ya kuskure — duk abin da Allah Ya yi shi ne daidai. Kuma yau kada ta dame su, abu idan ya fara, karshensa ake dubawa. Allah Ya sa mu yi karshe mai kyau, Allah Ya sa mu gama lafiya.
Mun gode wa Allah da Ya ba mu dama muka yi shekarun da muka yi. Da Ya ba mu dama muka yi gine-gine da muka yi a gidan nan. Da Ya ba mu dama muka dawo da sarautar sunnar Sarki Halifa.
Kuma abin alfahari ne a gare mu, yadda Halifa ya yi sarauta da yadda ya bar ta, Allah Ya dora mu a kan wannan sunnar. Allah Ya sa yadda ya gama a kusanci da Allah mu ma mu gama a wannan kusanci.
Muna gode wa ‘yan uwa Musulmi adddu’o’i da aka yi na alkhairi shekara da shekaru. Muna roko a ci gaba da addu’a, wannan kasa tamu Kano, Allah Ya ba ta lafiya da zaman lafiya. Allah Ya yi muku albarka, Allah Ya raya ku, Allah Ya dawo wa da kasar nan da arzikinta. Allah Ya ba da shugabanni na gari. Wannan gida namu, Allah Ya kare mutuncinsa da martabarsa.
Kasarmu, Allah Ya dawo mana da ita. Allah Ya sada mu da alkhairi. Muna godiya. Mun gode. Mun gode. Mun gode.
Mun rabu da ku cikin farin ciki. Mun rabu da ku cikin kwanciyar hankali. Mun rabu da mu cikin godiya.
Subhanakallahumma wabihamdik. Asshadu Alla’ilahailla anta astagfiruKa wa’atubu ilaik. Wamatasha’una illa anyasha’Allahu rabbul alamin.
Wassalamu alaikum warahmatulLahi wabarakatuhu.