Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya ce duk wani mai ƙoƙarin ja da hukuncin Allah to ba zai taba wanyewa lafiya ba.
Sanusi II ya ce duk wani mai ƙoƙarin kawo tazgaro ga zaman lafiyar Jihar Kano a ƙarshe aniyyarsa ce za ta koma kansa.
SSarkin ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan rediyon Premier da ke Kano, inda yake roƙon al’ummar jihar su zamo masu bin doka da oda, da kuma gudun aikata abubuwan da ka iya ta da hankali.
- Dalilin da dimokuraɗiyya ta gaza kawo ci gaba a Afirka — Obasanjo
- Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe
Kazalika ya bayyana masu ƙalubalantar kasancewarsa Sarki a matsayin masu yaƙi da nufin Allah, kuma a cewarsa hakan ba zai taɓa zame musu alheri ba.
Da yake jan hankalin Kanawan kan muhimmancin haƙuri da addu’a a wannan gaɓar, Sarkin ya ce turka-turkar da ake ciki game da masarautar Kano ba wai don shi ake yi ba, sai domin yaƙi da hukuncin Allah.
“Muna kira ga al’umma da su zamo masu bin doka da oda. Wannan rigimar ba da ni ake yinta ba, yaƙi ne da abinda Allah Ya ƙaddara.
“Ina roƙonku ku yi haƙuri ku dage da addu’a. Tabbas Allah Zai ci gaba da goya wa adalai baya.
“Wuta kuma ita ce karshen duk wani mai shirya wa Kano maƙarƙashiya. Allah Ya hana shi zaman lafiya.
“Muna roƙon Allah Ya kare kasarmu da rayukanmu. Da yardar Allah duk mai kokawa da hukuncin Allah ba zai gama da duniya lafiya ba,” in ji shi.