✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na koya wa Ameachi darasi a siyasa —Wike

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce ya koya wa magabacinsa kuma Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi darasi a siyasa. Wike ta bakin mai magana da…

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce ya koya wa magabacinsa kuma Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi darasi a siyasa.

Wike ta bakin mai magana da yawunsa, Kevin Ebiri, ya ce duk da adawar Amaechi ga burinsa na siyasa, mutanen jihar sun zabe shi sau biyu a matsayin gwamna. —

“Sun ce ba za mu zama Gwamna ba, mun koya musu darasi a siyasa. A 2015, sun ce sai bayan ransu za mu yi Gwamna, amma ga shi na yi kuma ba su mutu ba.

“A 2019 ma sun ce ba za mu yi Gwamna ba tunda suna kan mulki, amma na ce ba ku isa ba, Allah ne Mai iko. Mun riga mun ci su da yaki kuma su kanana kwari ne a siyasa,” inji sanarwar.

Wike ya kuma zargi Gwamnatin Tarayya da ba wa Amaechi kariya daga gurfanar da shi kan rashawa.

Ya ce hakan da Gwamnatin Tarayya ta yi na da ban tsoro kasancewar “ya kasa ba da bayanin Dala miliyan 308 daga cinikin kamfanin samar da wutar lantarki mallakar jihar da sauran muhimman kadarori lokacin da yake Gwamnan Jihar Ribas.”

Gwamnan ya ce kariyar da Amaechi ke samu ce ta sa yake yin kokarin bata sunan gwamnatin jihar ta hanyar “yin tasiri wajen zaben wanda za a tura a matsayin Kwamishinan ‘Yan Sanda da Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya a Jihar Ribas.

“Mutane sun ba ku dama. (Amaechi) Kun sayar da kadarorinmu kan $ 308 Million amma kuka ba mu $208,000,” inji shi.

Ya ce “Amma ina gargadin mutumin da ke jin yana da Shugaban Kasa, yana da sojoji, yana da ‘yan sanda. Kamata ya yi ku koyi darasi daga yanzu, cewa lokacin da Allah Ya bar ku babu abin da za ku iya sake yi.”

Amaechi shi ne Gwamnan Ribas tsakanin 2007 da 2015 kuma Wike na daga cikin mukarrabansa.

Wike ya yi aiki a matsayin Shugaban Ma’aikatan Amaechi kafin a nada shi Ministan a Ma’aikatar Ilimi, kafin su raba gari da juna ana gaba da babban zaben 2015.