Wanda ya zo na uku a zaben shugaban kasar Najeriya, Peter Obi na Jam’iyyar LP, ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben na ranar Asabar.
Peter Obi ya yi wannan ikirarin ne duk da cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar a safiyar ranar Laraba cewa Bola Tinubu na Jam’iyyar APC mai mulki ne ya lashe zaben.
Sakamakon zaben da INEC dai ta sanar ya nuna Tinubu ya yi nasara da kuri’u 8,794,726, kuma hukumar har ta mika masa takardar shaidar zama zababben shugaban kasa a ranar Laraba.
Sakamakon zaben ya nuna dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ne ya zo na biyu a zaben da kuri’a 6,984,520.
Peter Obi na Jam’iyyar LP ne a matsayi na uku da kuri’a, 6,101,533, wanda ya zo na hudu kuma shi ne tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, da kuri’u 1,496,687.
Amma a taron ’yan jarida da ya gudanar a ranar Alhamis, peter Obi ya ce shi ne ya ci zaben kuma yana da hujjojin da ke tabbatar da cewa ya kayar da da Tinubu.
A cewar Peter Obi, zaben da INEC ta gudanar a ranar Asabar shi ne mafi muni a tarihin Najeriya, kuma bai kai mafi karancin abin da ake tsammani ba.