Mista Eke Emmanuel, wani mai sana’ar wankin mota a yankin Lugbe da ke Babban Birnin Tarayya Abuja ya ce sana’ar ta gama yi masa komai a rayuwa.
Mai kimanin shekaru 36 a duniya, matashin yayin wata hirarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja ya ce an fi samun alheri a sana’ar lokacin damina, kasancewar akasarin direbobi na son ganin motocinsu cikin tsafta.
- Tsohon Kwamishinan Kano ya soki Ganduje kan taka hoton Kwankwaso
- ’Yan sanda sun dawo da dokar hana taro a Kano
Ya ce, “Idan aka yi ruwan sama, tabon da ke fallatsa da kuma yayyafin da ke sauka a jikin motoci kan sa su baci da wuri.
“A irin wannan lokacin, masu mota kan ziyarcemu a kai a kai. Na kan sami kusan N5,000 a kullum, da sana’ar nake ciyar da iyalina,” inji shi.
A cewar Mista Eke, abubuwan da ake bukata domin fara sana’ar sun hada da jarin kudi, wuri da zai kasance fuskar jama’a sai kuma yin rijista don kaucewa matsaloli daga mahukunta.
Ya kara da cewa, zai yi kyau mai son shiga sana’ar ya buga katinsa na kasuwanci domin mutane su ji dadin dawowa wajensa.
Sai dai a cewar Mista Eke, babban kalubalen sana’ar tasu bai wuce yadda wasu abokan huldarsu ke da wuyar sha’ani ba, ta yadda ba a iya yi musu gwaninta.
Kazalika, ya ce tashin farashin sinadarin da suke amfani da shi wajen wanke motocin shima yana kawo wa sana’ar tasu tarnaki.
Ya ta’allaka tsadar kan yawan kudaden da ake kashewa wajen shigo da sinadaran daga kasashen waje.