✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na kan ji takaici duk lokacin da aka kai wa ’yan Najeriya hari —Buhari

“A matsayi na uba, nima na kan ji radadi duk lokacin da yara suka fada irin wannan yanayin

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ya kan ji matukar takaici a duk lokacin da aka sami hari sakamakon matsalar tsaro a Najeriya.

Buhari, wanda ya bayyana hakan ranar Alhamis a sakonsa na Kirsimeti ga Kiristocin Najeriya ya kuma yi kira ga ’yan kasar da su kara jajircewa wajen taimaka wa sojoji da sauran jami’an tsaro a yakin da suke yi da ’yan ta’adda.

Shugaban ya ce, “Ba zai yiwu na yi watsi da nauyin da ya rataya a wuyana ba wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasa.

“Na kan ji matukar takaici a duk lokacin da aka sami wani kalubalen tsaro a kasar nan.

“Na ma fi jin takaici idan matasa, musamman yara ’yan makaranta abin ya shafa duk da cewa su ne ba su ji ba, ba su gani ba.

“A matsayi na uba, ni ma nakan ji radadi duk lokacin da yara suka fada irin wannan yanayin na ayyukan ’yan ta’adda, makiya zaman lafiyan al’umma.

“Ina kira ga ’yan uwa ’yan kasa da su ci gaba da ba jami’an tsaronmu karin lokaci, hadin kai da kuma goyon baya ta hanyar ba su bayanan tsaron da suke bukata wajen kakkabe ayyukan ’yan bindiga, masu tayar da kayar baya da sauran bata-gari domin kawo karshen kalubalen tsaron kasarmu,”  inji Buhari.

Shugaban ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba sojoji duk irin taimakon da suke bukata, tare da rokon su kan su kara jajircewa wajen kawo karshen matsalar da ke kara kamari a kullum.