Wata likita da ta kafa cibiyar koyar da mata sana’o’in hannu, Dokta Larai Aliyu Tambuwal ta ce, ta kafa cibiyar ce don magance zaman banza a tsakanin mata. Likitat ta kafa cibiyar koyar da mata sana’o’in ne a gidanta da ke Unguwar Nakasarin Ardo a Karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu da ke Jihar Sakkwaton a watan Janairun bana.
Ta samar da kayayyakin aiki a cibiyar don horar da teloli da koyar da mata yin man shafawa da sabulu da man wanke kai da kayan kamshi a cibiyar da ke karkashin Kungiyar Matan Nakasari (NAWARDA).
Ta ce, kungiyar an kirkiro ta ce don tallafa wa kai a tsakanin mata da yin zumunci a tsakanin mambobi da wayar da kai dangane da lamuran yau da kullum tare da ilimantar da juna game da zamantakewa da kiwon lafiya da koyar da sana’a don rage zaman banza tare da karfafa dogaro da kai.
Ta ce sauran ayyukan kungiyar sun hada da warware matsalolin da suka shafi addini da kula da lafiyar mata da kananan yara da matasa ta hanyar nema musu kariya daga cuta da ba da hakki na tarbiyya da samar da abinci da sutura da hana zaman banza da shaye-shaye da abin da suke haifarwa.
Dokta Larai Aliyu Tambuwal ta shaida wa Aminiya cewa makasudin kafa cibiyar shi ne kawar da zaman banza a tsakanin mata da matasa.
“Cibiyar ta yi rajistar mata kusan 400 ana koyar da su dinki da hada kayan kamshi na jiki da daki da man daki da sauran kayan kamshi,” inji ta. “A kwanan nan ne muka yaye mata 150 da suka koyi yadda ake hada kayan kamshi da wadansu 50 da suka koyi dinki, dukkansu mun raba musu kayan da suka koya don dogaro da kai,” inji Dokta Larai.
Ta ce kwalliya ta biya kudin sabulu, saboda mafi yawan wadanda suka koyi sana’o’in a yanzu suna cin amfaninsu musamman masu yin kayan kamshi, suna kai hajojinsu zuwa kasuwannin kauye da gidajen matan aure kuma suna samun abin kashewa daidai gwargwado.
“Domin su kara rike sana’o’insu muna gabatar musu da kasidu a lokacin horarwa. Muna kai gudunmawa ga matar da ta samu haihuwa da raba kayan masarufi a farkon watan Ramadan da sayen kayan masarufi don neman riba a gaba. Mun fito da cibiyar ce ganin yadda gwamnati take yin ko oho ga talakawa, musamman mata. Muna son a rage dogaro da gwamnati kacokan, komai sai gwamnati ta yi, kai dai yi iya naka sai gwamnati ta tallafa. Masu hannu da shuni kuma su rika shiga cikin irin wannan shiri su saka jari. In maza suka ba da hadin kai mata za su rage masu wani nauyi, don tallafa wa juna. Bukatarmu wadanda muka horar kada su yi wasa,” inji Dokta Larai Tambuwal.