✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na hannun daman Amaechi ya sauya sheka zuwa PDP

Jim kadan da sauya sheka zuwa PDP, Finebone ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike, babban dan adawar Amaechi

Chris Finebone Babban na hannun daman tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya sauya sheka daga Jam’iyyar APC zuwa PDP.

A safiyar Juma’a ne Finebone wanda ya dade yana aiki a matsayin Kakakin Amaechi ya tabbatar wa Aminiya cewa ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar PDP mai mulkin Jihar Ribas.

Sai dai bai bayyana dalilinsa na barin APC ba, jam’iyyar uban gidansa, zuwa PDP ba, jam’iyyar Gwamnan Nyesom Wike, babban dan adawar Amaechi.

Sauya shekar tasa na zuwa ne a yayin da ake shirin kulla yarjejeniya tsakanin APC da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike.

Finebone ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ,“Dan takarar Gwamnan Jihar Ribas na Jam’iyyar PDP, Similanayi Fubara, dan uwansa ne; a san hakan a samu kwanciyar hankali!”

Jim kadan da sauya sheka zuw PDP, Finebone ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a gidansa da ke Fatakwal tare da tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Davis Ikanya, da kuma ɗan takarar gwamnan.