Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta gaji manyan matsaloli a hannun magabacinsa, tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Tinubu ya koka da yadda Najeriya ke fama da tabarbarewar ababen more rayuwa da samar da wutar lantarki da kuma ayyukan noma.
- Yadda muka tsinci kanmu a ranar farko ta yajin aikin NLC — Kanawa
- Yadda yajin aikin NLC ya kasance a Bauchi da Kano
Tinubu ya bayyana hakan ne a daren ranar Litinin, a birnin Makkah na kasar Saudiyya, yayin da yake ci gaba da tattaunawa da shugabannin kasashen Larabawa kan samar da ababen more rayuwa na biliyoyin daloli daga Bankin Ci gaban Musulunci.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale, ya sanar a wannan Talatar, Tinubn, ya ce duk da mummunan yanayin da ya karbi kasar ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ya yi abun a zo a gani.
“Najeriya ita ce fitilar da za ta haskaka Afirka. Kuma da zarar Afirka ta samu haske, duniya za ta zama wuri mafi haske ga dukkan dan Adam.
“Mun kuduri aniyar samar da makoma ga matasanmu. Zuba jari a Najeriya zai kasance wuri mafi riba a duniya. Kudaden masu zuba hannun jari za su rika tafiya cikin sauki a kasarmu.
“Muna da babban gibi a ababen more rayuwa a tashar jiragen ruwa, samar da wutar lantarki, da kayayyakin aikin gona da za su ba da damar samar da abinci a kasarmu, wannan koma baya na barazana ga kasarmu.
“Mun gaji manyan basussuka. Ba mu da wani uzuri. Akwai fannoni da dama na saka hannun jari. A matsayinku na masu abota da Najeriya kuma masu taimako za mu so ku hada kai mu don samar da mafita,” in ji shugaban.
Da yake karin haske kan sauye-sauyen tattalin arziki, Mataimakin Shugaban Bankin Ci gaban Musulunci ya ce kasashen duniya masu kudi sun sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya.
A karshe shugaban ya mika godiyarsa ga mahukuntan bankin ci gaban Musulunci, yayin da ya yi alkawarin jajircewa na ganin an samu amincewar masu zuba jari, kamar yadda ya yi a Jihar Legas lokacin da yake gwamna.
Wakilan Najeriya da suka halarci taron a Makkah sun hada da: Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi; Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina; Gwamna Umar Bago na Jihar Neja; Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu da sauransu.