✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda yajin aikin NLC ya kasance a Bauchi da Kano

NLC da TUC sun tsunduma yajin aikin ne a daren ranar Litinin.

Ma’aikata a Jihar Bauchi sun bijire wa yajin aikin da kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC suka shiga a wannan Talatar.

Wannan mataki na ’yan kwadagon na zuwa ne sakamakon abin da suka kira gazawar gwamnatoci a dukkan matakai na rage radadin ma’aikata a dalilin cire tallafin man fetur da kuma cin zarafin shugaban kungiyar NLC da jami’an tsaro suka yi a Jihar Imo.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa harakokin ilimi, kasuwanci, lafiya da kuma bankuna sun samu cikas.

A makarantar karamar sakandare ta Government Day da ke Gwallameji da Sa’adu Zungur a Bauchi, dalibai da malamai sun gudanar da aikinsu kamar kullum.

Malam Abubakar Sadiq wanda malami ne a makarantar, ya ce ba su samu umarni a rubuce game da yajin aikin ba.

“Muna karkashin gwamnatin jiha ne kuma har yanzu muna jiran sanarwar da za ta sanar da mu shiga yajin aikin.

“Ba za mu iya tafiya yajin aiki ba tare da sanarwa ba, don haka ayyukan ilimi na yau da kullum za su ci gaba da gudana a makarantunmu.”

Kazalika ayyukan yau da kullum a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Yelwa da sauraren asibitoci na aiki a jihar.

Sai dai yajin aikin ya gurgunta ayyukan a makarantu, asibitoci, bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a Kano.

NAN ya ruwaito cewa, ma’aikata kalilan ne suka shiga yajin aikin a ofisoshin Gwamnatin Tarayya da na gwamnatin jihar.

Lamarin dai ya sanya wasu malamai suka kora daliban makarantun firamare da sakandire gida.

Haka kuma, yajin aikin ya sanya soke jarrabawa wasu dalibai a Jami’ar Bayero da ke Kano, yayin da dalibai wasu sun zana tasu jarrabawar a wasu sashen ilim.

Kazalika, an kuma rufe wasu daga cikin bankuna da wasu ma’aikatun jihar.

Shugaban Kungiyar Kwadago a jihar, Kabiru Inuwa ya bayyana cewa suna bakin kokarinsu wajen ganin mutane sun bi umarnin yajin aikin.

Ya ce aikin masana’antu ya tsaya da kashi 75 cikin 100 a jihar.