✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na ga jirgi

Wani Banufe ne ya je Kano, to sai hanyarsa ta kai shi kusa da filin jirgin sama. Shi bai saba ganin jirgi kasa-kasa haka ba…

Wani Banufe ne ya je Kano, to sai hanyarsa ta kai shi kusa da filin jirgin sama. Shi bai saba ganin jirgi kasa-kasa haka ba a Bidda, ga jirage nan sai wucewa suke kasa-kasa. Yana so ya daga kai ya gani amma yana tsoron za a yi masa kallon dan kauye. Sai ya tambayi bandaki zai kewaya, ya dauki buta ya shiga ya kulle. Ya ajiye butar a gefe, ya daga kansa sama yana kare wa duk jirgin da zai wuce kallo. Can ya fito ya yi hamdala, sannan ya ce a ransa: “Yau kam na ga jirgi.”
Daga Abdullahi Musa Hadeja, 07066180429