Alhaji Sani Mu’azu, jarumi ne da aka dade ana damawa da shi a masana’ntar fim ta Kannywood da Nollywood, sannan dan jarida ne kuma basarake mai rike da sarautar Makaman Jos. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana yadda ya fara harkokin fim da burinsa na gaba:
Za mu so mu ji tarihin rayuwarka?
To, ni dai an haife ni ne a garin Jos, a 1960. Na yi makarantar firamare da sakandare duk a Jos. Na yi karatun aikin jarida a Makarantar Koyon Aikin Jarida da ke Legas. Daga nan na dawo Jami’ar Jos, na karanta aikin jarida.
- ‘Ambaliya ta yi ajalin mutum 134 da dukiyar N1.5trn a Jigawa’
- An kama motoci makare da makaman da za a kai Katsina a Legas
Na fara aikin jarida a Tashar Talabijin ta kasa (NTA) da ke Jos. Na fara aiki da gabatar da shirye-shirye kafin a bude tashar talbijin ta Gwamnatin Jihar Filato ta PRTb. Daga nan na koma wannan tasha, a lokacin tana PTV. Mu ne ma’aikata na farko a tashar a 1992. A 1986, sai hankalina ya karkata ga harkar fim.
A lokacin akwai wani babban fim da aka yi a nan Jos, daga Hollywood mai suna Soweto. A lokacin ana kan gwagwarmayar neman ’yancin kasar Afirka ta Kudu a 1986. Wannan fim ya shafi wannan gwagwarmaya ta neman ’yancin Afirka ta Kudu. Ba su samu damar yin wannan fim ba a can kasar, shi ne suka zo nan Jos aka yi wannan fim kuma na shiga ciki. Wannan fim yana daya daga cikin abin da ya bude mani ido a harkar fim .
A 1992 na yanke shawarar ajiye aikin gwamnati. Daga nan muka bude wani kamfanin harkar sadarwa mai zaman kansa ni da wani maigidana.
Daga nan kuma a 1993 na yanke shawarar kafa kamfanina na harkar sadarwa, mai suna Lenscope Media a nan garin Jos.
Amma ban samu rajistar kafa kamfanin ba, sai a 1995. Kuma har zuwa wannan lokaci, ina aiki a karkashin wannan kamfani ne.
A matsayinka na daya daga cikin wadanda suka assasa harkar finafinan Hausa, yaya ka tsinci kanka a wannan harka?
Game da assasa harkar finafinan Hausa, wani abu ne wanda ba zan ce ga yadda na shiga ba. Domin harkar finafinan Hausa ta zo ta tarar da ni ne a harkar fim. Kamar yadda na fada maka, a tarihina, na fara harkar finafinai tun a 1986, har zuwa 1990.
Kuma a lokacin dukkan finafinan da muke yi, muna yin su ne a karkashin gidan talabijin. A lokacin babu Masana’antar Kanywood ko Nollywood. A lokacin na shiga wani babban shiri na Turanci da ake nunawa a talabijin, mai suna Behind the Clouds, wanda a lokacin duk Najeriya ana kallon wannan shiri a tashar NTA.
Haka kuma, na shiga wani shiri mai suna Shadows a matsayin dan wasa. Kuma wadannan shiryeshirye duk na Turanci ne.
Sannan mun hadu a NTA muka kirkiro wani shiri na Hausa, mai suna Bakandamiya. A wannan shiri akwai Auwalu Salihu da Magaji Mijinyawa da sauransu. A hankali finafinan da muke yi a gidan talabijin ne suka zamo silar yadda aka yi aka kirkiro Masana’antar Kanywood.
Domin ko a Kano, idan ka duba wadanda suke yin shirye-shiryen wasan kwaikwayo a gidajen talabijin, su ne suka shirya fim din Hausa na farko na Kanywood mai suna Turmin Danya. Mu ma akwai wadanda muka yi a nan Jos. A lokacin na yi finafinan Hausa irin su Dadin Duniya da sauransu. A haka muka tafi har aka kai ga kafa Masana’antar Kanywood. A lokacin da aka zo kafa wannan masana’anta, mu ne dai muka tsaya wajen kafuwar ta.
Kuma mu ne muka mayar da Kano ta zama cibiyarta, saboda can ne kasuwar finafinan take. Ana shirya wadannan finafinai a Kaduna da Jos da Kano. Amma ko da ka shirya fim a Kaduna ko Jos, dole Kano za ka je ka sayar, don haka Kano ta zama cibiyar wannan masana’anta.
A lokacin da aka zo kafa kungiya ta farko, wadda ta hada dukkan ’yan fim mai suna MOPPAN, shugaban wannan kungiya na farko shi ne Abdulkarim Muhammed ni kuma na zama Sakataren kungiyar. Bayan Abdulkarim Muhammed ya gama wa’adinsa, sai aka sake sabon zabe, inda aka zabe ni a matsayin sabon Shugaban kungiyar.
Bayan na gama wa’adina, sai aka zabi Farfesa Umar Faruk Jibrin. Da ya gama aka zabi Alhaji Abdullahi Maikano, yanzu kuma Dokta Sarari ne shugaban. Ka ga idan ka duba, cikin shugabannin Kanywood baki daya, ni ne shugaba na biyu tun farkon kafa kungiyar. A cikin wadannan shekaru da nake magana, situdiyo dina ya zama kamar wajen da ake horar da matasa wannan sana’a ta fim. A cikin wadanda suka yi aiki a situdiyo din, wasu sun zama jarumai wasu sun zama editoci wasu sun zama masu kyamara, wasu sun zama furodusoshi da sauransu. Ba zan iya kirga yawan mutanen da na horar ba a wadannan shekaru da suka gabata.
Wane fim ne ka fara yi ko ka fara fitowa?
Shi ya sa na ce maka, mu mun fara ne a talabijin. Mun yi wasannin kwakwayo da yawa a talabijin. Kuma wasannin kwaikwayon da muka yi a talabijin wasu ma sun kare a kasuwa. Kuma kafin a fara Kanywood, finafinan da na fito, sun haura 40.
Ni ba sabon shiga ba ne, da zan ce ga fim din da na fara. Yanzu idan na ce zan yi maganar finafinan da na fito a Kanywood, sai dai a yi maganar daruruwa.
A cikin dukkan finafinan da ka yi ko ka fito, wanne ne ya fi burge ka?
Wato ayyukan na canzawa kuma kowane allazi da nasa amanu. Zamani yakan zo, a wani zamani za ka ga kamar fim ya fi zama fitacce. Amma da yake Allah Ya yi mani baiwa da dogon zamani, domin har yanzu ana tafiya da ni, sai ka ga wani zamani ya fito da wani sabo.
Don haka, da wuya in ce maka ga kwai wasu finafinaina da mutane suke magana a kansu. Misali a nan Arewa, na dade ban yi fim din da ya samu karbuwa ba kamar fim din Kwana Casa’in da tashar talabijin ta Arewa 24 take nunawa, wanda fim ne mai dogon zango, kusan ko’ina ka shiga za ka ji ana labarinsa.
Yanzu kusan sunana ya tashi daga Sani Mu’azu, yana neman ya koma Bawa Maikada. Mutane maza da mata ko a ce Gwamna ko a ce His Excellency ko a ce Bawa Maikada. Wannan fim ya karbu sosai a wajen jama’a. Amma akwai wasu finafinai da na yi a ’yan kwanakin nan. Akwai boiceless wanda kamar na Turanci ne, amma da Hausa muka yi shi.
Wannan fim ya samu karbuwa kuma ya samu kyaututtukan karramawa. Akwai wasu finafinan da na yi, wadanda ba su fito ba, da nake matukar ji da su. Saboda haka, da wuya in ce maka ga fim daya, da shi ne ya fi burge ni a cikin finafinan da na yi.
Ka fito a matsayin Gwamna a fim din Kwana Casa’in, me ya sa aka zabe ka don ka taka wannan rawa?
Wadanda suka zabe ni, su ne ya kamata a tambaya. Amma ina kyautata zaton sun zabe ni saboda suna ganin ina da izza da cika ido. Kuma ni a yanayina, duk wasan da nake yi, ina yi ne kamar haka yake. Allah Ya ba ni wadannan abubuwa. Don haka, sau da yawa fitowar da ake ba ni a fim, za ka ga ana yin la’akari ne da wadannan abubuwa da Allah Ya ba ni.
Mai yiwuwa shi ne suka duba, suka yi la’akari da shi. Don ba ni ne na nemi su sanya ni ba, gayyata ta suka yi lokacin da suke tantance ’yan wasan da za su yi wannan fim. Sun gayyace ni, na je Kano suka ce akwai fitowar da suke ganin zan iya yi a wannan fim. Ina zuwa wajen ban dade ba, suka ce in tafi kawai an gama zan iya.
Me ya sa ka amince ka fito a wannan matsayi na Gwamna Bawa Maikada?
Dalili na farko shi ne, harkar fim ba na daukar sa a matsayin wasa. Domin fim harka ce ta isar da sako. Kuma na kalli wannan fitowa ta dan siyasa wanda yake amfani da bakar hanya, wajen isar da manufarsa ta siyasa.
Mafi yawan masu jefa kuri’a ba su san ’yan siyasa suna yaudarar su ba ne. Ba su san ’yan siyasa suna wasa da hankalinsu ba ne. Sai na ga dama ta samu da zan fito da irin illar da irin wadannan ’yan siyasa suke yi.
Na nuna wa duniya cewa, yawancin ’yan siyasar nan, ba wadanda za a amince da su ba ne. Idan sun ce maka ga abin da suke nema, to yawanci aljihunsu suke so su raya, ba ci gaban jama’a ba.