✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na ci na sha da sana’ar like robobi – Malam Murtala

Aminiya: Za mu so ji takaitaccen tarihinka? Malam Murtala: Sunana Murtala Lawal, an haife ni kimanin shekaru 52 da suka wuce, a unguwar Mannar Kadabo…

Aminiya: Za mu so ji takaitaccen tarihinka?

Malam Murtala: Sunana Murtala Lawal, an haife ni kimanin shekaru 52 da suka wuce, a unguwar Mannar Kadabo da ke cikin garin Katsina. Na yi makarantar allo na kuma yi ta firamare, amma daga nan ban ci gaba ba.
Aminiya: Me ya sa ka bar karatun boko?
Malam Murtala: To, kasan shiririta irinta yaro,musamman a wancan lokaci. Ni dai sana’ar da na gani ana yi gidanmu ita tafi daukar hankalina. Na tashi a gidanmu na taras ana sana’ar kira. Ana kera tukwanen karfe da galmar shanu da ake amfani da ita wajen aikin gona da sauransu.
Aminiya: Ga shi mun taras kana wata sana’ar wadda ba kira ba?
Malam Murtala: – Eh, haka ne. Wata baiwa ce da Allah Ya ba ni ta wannan sana’a ta Nani ko liki ko kuma makaneza ko wandar roba, wato gyaran tankin ruwa na roba da danjar mota ko ta babur, da duk wani abin da ya shafi roba cikin yardar Allah zan iya gyara shi kuma ya zauna daidai kamar bai taba lalacewa ba. Kuma wannan baiwa Allah Ya bani ita ne sama da shekara talatin ke nan.
Aminiya: Wadanne irin kayan aiki kake wannan sana’ar da su?
Malam Murtala: Ai kayan makera ne nake amfani da su. Saboda ka ga akwai awartaki da almakashi da tsinkuna da kuma murhun hura wuta na zamani wanda ake yi da fankar da aka lullube da kasa da abinda ake juya fankar wanda yake karfen tayar babur ne bayan sandar da ke kai iskan fankar ga can, inda ake zuba gawayi ana sake hura shi don ya ci gaba da ba da wutar da zata sanya karfen yin nanin yayi zafi, maimakon tsohuwar hanyar da ake yin zugar wutar makera a da, saboda aikin da wuta ake yinsa. Kuma ina tabbatar maka da cewa, duk irin yadda tankin da ake ajiyar ruwa ya fado kasa ya farfashe, idan Allah Ya so na gyara shi ba dai za a ga digon ruwa ya zubo ba.
Aminiya: Shin akwai wanda ya koya maka wannan sana’ar?
Malam Murtala: Akwai wanda ya koya mani kuma yana Kano ne. Domin na bar gida zuwa Kano wajen yin kirar wadannan tukanan karfe. To a can ne na fara koyonta wajen wani ubangidana. Allah kuma ya yarda da al’amarin.
Aminiya: Wace irin riba da ake samu cikin wannan sana’a?
Malam Murtala: kwarai kuwa. Ni a yanzu ai wannan sana’ar tafi zuma zaki a wajena. Saboda na ci na sha da ita. Bari na takaita maka duk wani abinda sana’a zata yiwa mutum ni wannan sana’ar tayi mini. Farko dai bani mantawa lokacin da na taba sayen tufafi na kaiwa tsoffina a lokacin irin albarkar da suka sanya mani har gobe tana bina. Kuma duk da ni ban ci gaba da karatun boko ba,a yanzu nike biya wa yara kudin makaranta ta Islamiyya da ta boko kuma duk da wannan sana’ar, bayan muhalli da kuma rikon iyalina da wasu daga cikin ‘yan-uwana da nike taimakawa. Kai wannan sana’ar ta taimaka mini na shiga harkar kasuwanci, domin a yanzu haka ina sayen babura da motoci, ina sayarwa.
Aminiya: Akwai wani abinda wannan sana’ar ta janyo maka wanda baka mantawa da shi?
Malam Murtala: Farko dai akwai sanya albarka da iayena suke mini. Sai kuma wata kyauta da wani kwamishina ya taba yi mini ta wasu makudan kudi dalilin wannan gyara. Har’ ila yau, har ya zuwa yanzu maganar nan da muke yi, babu wani wanda na taba yi wa gyara ya mayar mani da sunan bayyi ba.
Aminiya: Kana yunkurin koyawa wani ko da cikin ‘ya’yanka wannan sana’ar?
Malam Murtala: Kafin nawa yaran su tasa. Na koya wa matasa da yawa wadanda suma wasu daga cikinsu sun koyar da wasu. Ka ga ashe sai dai kawai na ce, Alhamdulillahi.
Aminiya: Wane jan hankali zaka yi ga matasa?
Malam Murtala: Farko dai ina kira ga masu sana’ar hannu da su tsare gaskiya, kuma su yi kokarin cika alkawari idan sun dauka. Su rike sana’a komai kankantarta, wata rana ita ce babba. Ka ga yanzu idan zan samu tallafin kayan aiki, to ina tabbatar maka zan iya yin tanki ko bambar mota da sauransu. Kuma mu yi kokarin hada kai ta hanyar kafa kungiya domin ta kungiya ne zamu iya samun duk wani tallafin da muka nema daga gwamnati.