Tsohon kocin kulob din Giwa FC da ke garin Jos a Jihar Filato Aminu Musa wanda yanzu ya sanya hannu a kan kwantiragin shekara 2 a matsayin mataimakin kocin kulob din Enyimba da ke garin Aba a Jihar Abiya, ya bayyana ya amince ya zama kocin kulob din ne don yana da burin kafa tarihi.
Koci Aminu ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a garin Jos a ranar Litinin da ta gabata.
Aminu wanda tsohon kocin kulob din Mighty Jets da ke Jos ya ce, ya fara aiki da kulob din ne a makon jiya, kuma kulob din Enyimba ya neme shi sakamakon namijin kokarin da ya yi a lokacin da ya jagoranci kulob din Giwa FC a gasar firimiya da aka kammala a watan Nuwamban bara.
Ya ce: “A kullum burina in yi aiki da kulob din Enyimba, domin shi ne babban kulob mafi daukaka da samun nasara a Najeriya, zamana kocin kulob din ya sanya ni farin ciki da kuma alfahari. Na kuma amince in yi aiki da kulob din ne don bada gudunmuwar da za ta sanya in kafa tarihi a kulob din.” Inji shi.
A karshe ya bukaci ’yan wasa da magoya bayan kulob din da kuma sauran jami’an kulob din da su ba shi ciakken hadin kai don ganin ya cimma burinsa na ajiye tarihi a kulob din.
Na amince in yi aiki da Enyimba don in kafa tarihi ne – Koci Aminu
Tsohon kocin kulob din Giwa FC da ke garin Jos a Jihar Filato Aminu Musa wanda yanzu ya sanya hannu a kan kwantiragin shekara 2…