✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – Matashi

Kwamishinan ya ce za a miƙa waɗanda ake zargin zuwa kotu da zarar sun kammala bincike.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, ta kama wani matashi tare da wasu mutum uku kan zargin safarar harsasai daga Jos zuwa Abuja.

Matashin ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun biya shi Naira 50,000 domin ya karɓo harsasai daga Jos zuwa Abuja.

“Ni mazaunin Abuja ne. Makonni biyu da suka wuce, wani mutum ya aike ni domin karɓo masa harsasai a Jos zuwa Abuja.

“Ya tabbatar min babu wata matsala da zan fuskanta, amma a hanya jami’an tsaro suka kama mu ni da wasu mutum uku,” in ji matashin.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, yayin da yake holen waɗanda ake zargi, ya ce an kama su ne bayan samun rahoton sirri kan ayyukansu.

“Mun kama waɗanda ake zargin ne bayan samun sahihan bayanan sirri.

“Rundunar na ci gaba da bincike, kuma da zarar an kammala, za a miƙa su zuwa kotu domin fuskantar hukunci.”