✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

N5,000 muke karba harajin ajiyar jiragen sama a Najeriya tun 2002 —Gwamnati

Hukumar Sufurin Jiragen sama ta Najeriya (NCAA) da Hukumar Filayen Jirgin sama (FAAN) ta ce batun kara kudin harajin sauka da adana jirgin saman da…

Hukumar Sufurin Jiragen sama ta Najeriya (NCAA) da Hukumar Filayen Jirgin sama (FAAN) ta ce batun kara kudin harajin sauka da adana jirgin saman da ake cewa sun yi ga kamfanonin jiragen cikin gida da na kasshen waje jita-jita ce.

Babban Daraktan NCAA, Kyaftin Musa Nuhu ne ya bayyana haka a Filin Jirgi na Murtala Mohammed da ke Legas, yayin rangadin ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed a tashar.

Kyaftin din ya ce rabon da hukumar ta yi karin haraji tun shekarar 2002 ne.

“A matsayina na Babban Daraktan NCAA, ban bai wa kowa umarnin karin haraji ba, a takaice ma rabon da mu yi wani kari tun shekarar 2002.

“Idan har shekaru goma da suka gabata muna karbar harajin N5,000, kuma har yanzu ma haka, ka lissafa irin asarar da muke yi saboda tashin farashin komai.

“Ba ma iya maida abin da muka kashe balle a yi maganar riba, amma wannan bai hana mu ci gaba da gudanar da ayyukanmu da kuma sanya tallafi ba.

“Hakan kuma ba yana nufin ba mu da matsalolin da muke fama da su, ga shi ba ma samun wani tallafi daga Gwamnatin Tarayya, sai dan abin da muka samu daga harajin.

Shi ma dai Shugaban FAAN, Kyaftin Rabiu Yadudu, ya ce tun a shekarar 2002 da suka kara harajin ga jiragen waje, sai a 2012 suka karawa na cikin gida.

“A wancan lokacin ana siyar da tikitin jirgi N6,000 ne, yaznu nawa suke siyar da shi? Amma duk wannan bai sa mun kara musu harajin ba,” in ji shi.

%d bloggers like this: