Matasa sama da miliyan daya ne suka yi rijistar neman aikin tallafin Gwamnatin Tarayya na N-Power cikin sa’a 48 bayan bude shafin a yanar gizo.
Ma’aikatar Jinkai da Jin Dadin Al’umma a cikin wani sako da ta fitar a daren Lahadi, 28 ga watan Yuni, ta ce “mun karbi rijistar sama da mutum 1,000,000 daga sassan Najeriya cikin kasa da sa’a 48”.
- N-power: Abun da ya kamata ku sani kafin fara rijista
- Gaskiya ne ba mu biya ‘yan N-Power 12,000 hakkokinsu ba —Gwamnati
Sanarwar ta kara da cewa ‘yan Najeriya masu shekaru 18-35, wadanda suka yi karatun boko da ma wadanda ba su yi ba, na iya neman gurbi a sabon tsarin na N-Power wanda zai mayar da hankali ga ayyukan gona.
“Adadin wadanda suka nemi gurbin a yanzu ‘yar manuniya ce na yawan matasan Najeriya da ke neman aiki, kuma suka yarda da tsarin N-power.
“Don haka ma’aikatar za ta yi hadin gwiwa da masu kula da shafinta na intanet domin ba wa masu neman gurabun aikin taimakon da suke bukata”, inji sakon.
Ma’aikatar ta kuma ce za a yi adalci a wajen tantance masu neman aikin, za kuma ta ci gaba da sanar da al’umma halin da ake ciki game da tsarin.