✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Myanmar ta daure ’yan kabilar Rohingya 112 saboda kokarin barin kasar

Daga cikin wadanda aka daure har da yara 12

Wata kotun kasar Myanmar ta daure Musulmai ’yan kabilar Rohingya kimanin su 112 bayan an kama su suna kokarin tsallakewa su bar kasar.

Bayanai sun ce daga cikin mutanen har da kananan yara 12.

Kotun, wacce ke zamanta a Bogale da ke Kudancin kasar, ta yanke wa mutanen hukuncin ne a ranar shida ga watan janirun 2023, kamar yadda kafar yada labaran gwamnati ta Global New Light ta rawaito ranar Talata.

An dai kama mutanen ne a watan Disamban bara, bayan an gano su a kan wani kwalkwale ba tare da wata takarda daga hukumomi ba, a cewar ’yan sanda.

Daga cikin yaran su 12, biyar ’yan kasa da shekara 13 wadanda aka daure shekara biyu, yayin da wadanda suka dara su shekaru kuma aka daure su shekara uku-uku.

Kafar yada labaran ta ce za a tisa keyarsu zuwa wata makarantar horar da kananan yara.

Sai dai duka manya daga cikin wadanda aka kama din sun sha daurin shekara biyar-biyar.

’Yan kabilar ta Rohingya, wadanda galibinsu Musulmai ne, a kan hana su takardar zama ’yan kasa da ma sauran hakkoki a kasar da galibin mazauna cikinta mabiya addinin Bhudda ne, inda ake zarginsu da cewa su bakin haure ne daga Kudancin Asiya.

Dubban daruruwan ’yan kabilar ne suka tsallaka domin yin gudun hijira zuwa makwabciyar kasar ta Bangledash a shekara ta 2017, bayan sojoji sun murkushe su.