An kashe wani fursuna tare da jikkata wasu mutane fiye da 60 bayan wata tarzoma ta barke a gidan yarin Yangon da ke Yammacin Myanmar.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Gwamnatin Mulkin Sojin kasar ta bayyana a ranar Lahadi.
Rikicin da ya barke a gidan yarin na Pathein ya fara ne bayan da masu gadi suka kwace wayar salula daga hannun wani fursuna a daren ranar Alhamis tare da daukar matakin ladabtarwa, in ji sanarwar da rundunar sojin ta fitar.
Kimanin fursunoni 70 ne suka tsere daga dakunansu tare da lalata dukiyoyi a safiyar Juma’a.
A cewar sanarwar, fursunonin sun yi amfani da sanduna da bulo da duwatsu wajen kai wa jami’an tsaro hari.
Hukumomin kasar dai sun yi kokarin shawo kan lamarin amma abun ya ci tura, inda suka yi amfani da karfi wajen kwantar da hankula.
Rundunar Sojin kasar ta ce an kashe fursuna guda daya a yayin rikicin, sannan fursunoni 63 sun jikkata tare da ’yan sanda biyu da masu gadi tara.
A makon da ya gabata ne dai gwamnatin mulkin sojan kasar ta bayyana cewa za ta saki fursunoni sama da 7,000 domin bikin cika shekaru 75 da samun ‘yancin kai daga kasar Birtaniya.
Fiye da mutane 2,700 ne aka kashe tun bayan da sojoji suka karbe mulki, sannan sama da mutane 13,000 ake tsare da su a wani mataki na murkushe ‘yan adawa a cewar wata kungiyar sa ido a kasar.
A watan Yulin shekarar da ta gabata ne gwamnatin kasar ta zartar da hukuncin kisa kan fursunoni hudu da suka hada da tsohuwar ‘yar majalisa Phyo Zeya Thaw da mai rajin kare demokradiyya Kyaw Min Yu.
Wannan dai shi ne karon farko da gwamnatin Myanmar ta yi amfani da hukuncin kisa a cikin shekaru kusan 30 da suka gabata, lamarin da ya janyo suka daga kasashen duniya.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce gidajen yarin Myanmar sun yi kaurin suna wajen azabtar da fursunoni.
Myanmar ta fada cikin rudani tun bayan hambarar da gwamnatin farar hula ta Aung San Suu Kyi a wani juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabrairun 2021, wanda ya kawo karshen wa’adin mulkin dimokuradiyya a kasar da ke kudu maso gabashin Asiya.