A makon da ya gabata ne shahararriyar mawakiyar fina-finan Hausa Rabi Mustapha ta kwanta dama bayan ta fama da jinya.
Wani fitaccen mawaki mai suna Alkhamis D. Bature Makwarari wanda suka yi aiki tare da marigayiyar a farko-farkon fara sana’ar fim din Hausa ya bayyana ta a matsayin jajirtacciyar mawakiya. “Kasancewar a lokacin da muka yi aiki tare ita kadai ce mawakiya mace, ta yi aiki ba dare ba rana wajen bunkasa harkar fim, domin a lokacin a koyaushe a cikin aiki take. Ta yi aiki ne ba don kudin da za ta samu kadai ba, ta kasance tana da sha’awar yin wakokin da kuma son dabbaka harshen Hausa” Inji shi.
Darakta Kamal S. Alkali ya ce ya kadu matuka da ya ji mutuwar mawakiyar, “ba ni kadai ba mutuwar ta jijjiga kowa a industiri.”
An haifi marigayiyar a Unguwar Yakasai cikin birnin Kano. Ita ce zabiya ta farko a cikin fina-finan Hausa, ta shafe shekara 19 zuwa 20 tana gudanar da wakoki a cikin fina-finai, baya ga haka takan fito a matsayin jaruma ko kawar jaruma ko uwa da sauransu a cikin fina-finai.
Marigayiyar bayan rera wakoki da take yi takan kuma rubuta. Wakokin da ta rera sun hada da wakokin fim din ‘Mujadala’ da ‘Badali’ da sauransu. Haka kuma ita ce ta fito a matsayin jarumar fim din ‘Ingiza Mai Kantu Ruwa’. Takan fito a wasannin kwaikwayo na Hausa mai suna ‘Ga-Ta-Nan-Ga-Ta-Nanku’ da gidan Rediyon BBC ya dauki nauyi.
Mawakiyar ta rasu ta bar mahaifanta da kuma dan ta mai suna Abubakar Saddik. Tuni dai aka yi jana’izarta kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.
Mutuwar mawakiya Rabi Mustapha ta jijjiga industiri
A makon da ya gabata ne shahararriyar mawakiyar fina-finan Hausa Rabi Mustapha ta kwanta dama bayan ta fama da jinya.Wani fitaccen mawaki mai suna Alkhamis…
