✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutuwa kofar shiga Aljanna ko wuta (2)

Abdussalam Aliagan, Masallacin NASFAT na Kasa da ke Abuja Fassarar Salihu Makera Godiya ta tabbata ga Allah, Wanda ya hukunta sunnonin rayuwa, Wanda babu wani…

Abdussalam Aliagan, Masallacin NASFAT na Kasa da ke Abuja

Fassarar Salihu Makera

Godiya ta tabbata ga Allah, Wanda ya hukunta sunnonin rayuwa, Wanda babu wani mai dauwama sai Shi Madaukaki. Wanda Ya sanya kasa abin wucewa takaitacciya ga dan Adam domin ya tashi ga raya ta da yi maSa ibada da sauran abubuwan da suke da alaka da rayuwar duniya zuwa rayuwar Lahira. Shi ne Wanda ya tilasta wa bayi mutuwa. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Shi ne fakon da babu fari ga farkonSa, kuma karshen da babu tukewa ga karshenSa, Mai raya rayayyu, kuma Mai kashe matattu.

Kuma na shaida lallai shugabanmu, masoyinmu mafi girmanmu maulanmu Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa wanda yake cewa: “Wanda duk ya mutu hakika Kiyamarsa ta tsaya” Ya Allah! Ka kara tsira da amince a gare shi salatin da za ta saukaka mana radadin mutuwa, amin.

Ya bayin Allah! Ku sani lallai duk yadda dare ya kai da tsawo babu makawa ga fitowar alfijir, kuma duk yadda mutum ya kai da tsawon rayuwa babu makawa zai shiga kabari. Ku sani lallai mutuwa takan zo bagatatan, shi kuma kabari ya gaskata aiki.

Ya bayin Allah! Za mu ci gaba da hudubarmu a yau kan mutuwa.

Ya bayin Allah! Kowane mutum mumini ne ko kafiri yana kin mutuwa, bai son a yi magana a kan mutuwa bai maraba da duk wani abu da zai jawo shi zuwa ga mutuwa, alhali mutuwa ba ta da magani, ita cuta ce da ba ta da magani.

Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai mutuwar nan da kuke gudu daga gare ta, to, lallai ita mai haduwa da ku ne sannan ana mayar da ku zuwa ga Masanin fake da bayyane, domin Ya ba ku labari ga abin da kuka kasance kuna aikatawa.” Kuma Ya sake cewa: “Rai bai san me zai aikata gobe ba, kuma rai bai san a wace kasa za ta mutu ba.”

Ya bayin Allah! Mutuwa wata aba ce da ba ta da makawa. Allah Madaukaki Ya ce: “Daga cikinta Muka halitta ku, kuma a cikinta za Mu mayar da ku, kuma daga cikinta za Mu fitar da ku a wani lokaci na daban.” Don haka ku yi tattali ga mutuwa ya ku bayin Allah don kada ta zo muku a auke.

Ya ku bayin Allah! Annabi Dauda (AS) ya tambayi Allah kan alamomin mutuwa. Sai ya mala’ikan mutuwa Azra’ilu ya amsa. Ya amsa wa Dauda (AS) lokacin da ya bukaci Allah kan alamomin da suke nuni da kusantowar mutuwa. Ya ce: “Shin bayanka bai tankware ba? Shin gashi kanka bai yi furfura ba? Shin makwabcinka bai mutu ba? To wadannan su ne alamomi uku, wadanda Allah Yake aikowa yau da kullum ga bayinSa, amma mutane da yawa suna jahiltar wadannan alamomi uku.

Abubuwan da suke bijiro wa mutum kafin ya mutu

a. Yawaitar shekaru da furfura suna daga cikin alamomin gabatowar mutuwa

b. Bijirowar aukuwar wasu abubuwa kamar hadarin mota ga mutum ko aukuwar cutar da za ta yi barazana ga rayuwarsa a karshe ta yi ajalinsa.

c. Mutum ya rika numfashi da kyar ya rasa karfin jiki.

d. Jiki ya yi sanyi saboda girma kamar sanyi a hannuwansa da kafofinsa

e. Mantuwa da rashin tunano abubuwa.

f. Numfashi sama-sama da rashin daidaiton jini a jiki.

g. Yawan gajiya da tsamin jiki

h. Rikicewa

Ya bayin Allah! Akwai abin ake kira da shidewa da gargara a lokacin da mutuwa ta kusanci ajalin kowane daya daga cikinmu. Bayin Allah! Ga duk mutumin da zai mutu yakan gani kuma ya san matsayinsa bayan ya mutu, shin Aljanna ce makomarsa ko wuta!

Allah Madaukaki Ya ce: “Idan mai aukuwa ta auku. Babu wani (rai) mai karyatawa ga aukuwarta. (Ita) mai kaskantawa ce, mai daukakawa. Idan aka girgiza kasa girgizawa. Kuma aka nike duwatsu nikewa. Sai suka kasance kura da ake watsarwa. Kuma kun kasance nau’i uku.  Wato mazowa dama. Mene ne mazowa dama? Da mazowa hagu. Mene ne mazowa hagu? Da wadanda suka tsere. Su wadanda suka tseren nan, Wadannan su ne wadanda aka kusantar. A cikin Aljannar ni’ima.” (K:56:1-12).

Ya bayin Allah! Ina horonku da riko da kyawawan ladubban Musulunci a lokacin mutuwar ’yan uwanku da gargararta. Ku rika lakanta musu kalmar shahada da sanya musu tunani da yin zikiri, amma kada ku umarci wani da cewa ya furta kalmar shahada. A’a ku rika ambatonta a wurinsa.

Allah Madaukaki Ya ce: “To don me idan rai ya kai ga makoshi (Kusa da mutuwa)?  Alhali kuwa ku a lokacin nan kuna kallo. Kuma Mu ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma ku ba ku gani. To don me in dai kun kasance ba wadanda za a yi wa sakamako ba? Ku mayar da shi (ran cikin jiknsa) har idan kun kasance masu gaskiya.” (K:56:83-87).

Wani ya rera cewa:

“Lallai Allah Yana da bayi masu hankali,

Sun saki duniya, suka ji tsoron fitina.

Sun duba cikinta yayin da suka gane,

Cewa ita ba wurin zama ba ne ga mai rai.

Sai suka sanya ta abin tuki,

Kyawawan kuma ayyuka a cikinta jirgin ruwa.” Ya bayin Allah! Ku sani lallai kyakkyawan karshe ta masu takawa ne. Lahaula wala kuwwata illa billahl aliyyil azim.

Huduba ta Biyu:

Godiya ta tabbata ga Mai cewa: “Ka ce, “Mala’ikan mutuwa da aka wakilta muku yana karbar rayukanku, sannan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku.”

Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, kuma na shaida lallai shugabanmu kuma maulanmu Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa.

Bayin Allah! Daga cikin alamomin mutuwa akwai daskarewar ido, wannan alama ce muhimmiya kuma tana nuni ne da fitar ruhi daga jiki. An karbo daga Ummu Salma (RA), ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya shiga ga Abu Salma alhali idonsa ya kafe, sai ya runtse shi (ya rufe shi), sannan ya ce: “Lallai idan aka karbi ruhi sai ido ya bi shi. Sai mutane daga iyalinsa suka rika ihu, sai ya ce: “Kada ku yi addu’a a kanku face da alheri, domin mala’iku suna cewa amin a kana bin da kuke cewa. Sannan ya ce, “Ya Ubangiji! Ka gafarta wa Abu Salma, Ka daukaka darajarsa a cikin masu kwanciyar kabari, Ka zama halifansa a bayansa cikin wadanda suka saura, kuma Ka gafarta mana da shi Ya Ubangijin talikai.”

Ya bayin Allah! Ku saurari abin da Shugaban Halitta, Masoyin Halitta ya ce; an karbo daga Dan Umar (RA) ya ce: “Na kasance tare da Manzon Allah (SAW), sai wani mutum ya zo masa daga cikin Ansar, ya yi sallama ga Annabi (SAW), sannan ya ce: “Ya Manzon Allah! Wane ne mafi falala a tsakanin muminai? Sai ya ce: “Mafi kyawun halinsu.” Ya ce: “Kuma wane mumini ne mafi hankalinsu?” Sai ya ce: “Wanda ya fi su tuna mutuwa, kuma ya fi su kyautata tattalin abin da ke bayanta. Wadannan su ne mafiya hankali.”

Daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Shekarun al’ummata yana tsakanin shekara sittin zuwa saba’in, kadan dinsu ne suka tsallake haka.”

Wani ya rera cewa:

“Lallai mutuwa da abin da ke bayan mutuwa, Da jahiltar abin da ke bayanta wa’azi ne da ya ishe mu.”

Wani kuma ya rera cewa:

“Na ga kabubura sai na kiraye su, Ina wanda ake girmamawa da wanda ake kaskantarwa?

Ina wanda ake wulakantawa duk da ikonsa, Kuma ina markazozi idan suka yi alfahari.

Na zaga cikinsu bai ga kowa ba,  Duk sun rube babu mai iya ba da labari.

Duk sun gushe babu mai ba da labari,   Duk sun mutu labarin ma ya mutu.

“Yak u wadanda suka yi imani ku bi Allah da takawa kuma ku fadi magana wadda take daidai. Sai Allah Ya kyautata ayyukanku kuma Ya gafarta zunubanku, wanda ya bi Allah da takawa hakika lallai ya rabauta da lada mai girma.

“Lallai Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da kuma ba abokin zumunta hakkinsa, kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da rarraba kan mutane. Yana yi muku wa’azi tsammaninku za ku yi tunani.”

Imam Sharafudeen Abdussalam Aliagan shi ne Babban Limamin Masallaicn NASFAT na Kasa da ke Abuja, kuma za a iya samunsa ta tarho mai lamba: 080347108620