Wani mutum da aka ayyana ya mutu har aka yi yawo da gawarsa tare da gangamin jana’izarsa shekara takwas da suka wuce a Zirin Gaza, ya dawo duniya tare da yin bazata ga wadanda suka yi ta kokarin ganin bayansa.
Mutumin mai suna Mohammed Sinwar, shi ne shugaban kungiyar masu gwagwarmaya da makamai ta Hamas a yankin Falasdinu.
- Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 10,000 a wata guda
- Gaza: Iran ta yi barazanar shiga yakin Isra’ila da Hamas
Wannan shugaba ya tsallake yunkurin hallaka shi da sojoji da kuma rundunar tsaro ta farin kaya da ‘yan leken asirin Isra’ila suka yi ta yi a baya, daga karshe aka ayyanna kashe shi a shekarar 2014.
A lokacin ‘yan Hamas sun fito da gawarsa an yi yawo kwararo-kwararo da ita ana kabbarori kamar yadda suka saba idan an kashe mata wani babba, sannan aka kuma binne shi.
Ashe ba shi ba ne kuma tsawon shekaru takwas Isra’ilan ba ta gane haka ba sai yanzu da aka soma wannan sabon rikicin, inda suka yi amanna yana da ransa kuma shi ya jagoranci kitsa kai harin ranar 7 ga watan Oktoba cikin kasar da wanda hakan ya yi sanadiyar hallaka Yahudawa kimanin 1,200 da kuma garkuwa da kimanin 420.
Ana zargin kungiyar ta rike su ne domin tilasta musayar fursunoni sama da 500 da take tsare da su a gidajen yarin Isra’ila kamar yadda Mohammed Sinwar ya kitsa a shekarar 2011, inda ya samu nasarar kubuto da Falasdinawa da yawa ciki har da yayansa Yahaya Sinwar.
Mohammed Sinwar na da matukar muhimmanci a tsarin shugabancin sojin kungiyar Hamas, a cewar shugaban Hukumar Leken Asiri ta Isra’ila MOSSAD.
“Shi ne na bakwai a jerin wadanda kasar Isra’ila ke nema ruwa a jallo a sahun manyan kungiyar Hamas” in ji shi.
Hare-haren bazatan da Hamas ta kai ta sama da ta ruwa da kuma ta kasa sun girgiza Isra’ila wacce ta yi ikirarin kariyar gagara-badau na ‘Iron Dome’ da suka ce ko guda ba zai ratsa kasar ba sai sun gan shi.
Amma kungiyar Hamas ta keta su da kuma hannun shugaban da aka ce ya mutu wanda ake zargin ya kitsa a maboyarsa a cikin rami.
Mohammmed Sinwar ya tsallake yunkurin hallaka shi sau shida a shekaru 20, a cewar Mista Solomon Romen, wani kwararre mai sharhi kan ayyukan leken asiri.
Sojojin Isra’ila sun rushe gidansu a watan Oktobar 2023, dalilin da ya shiga buyar da ta sa Hamas ta yi mi shi jana’izar karya don ci-gaba da yi mata aiki a karkashin kasa.
Isra’ila ta yi kaurin suna a kisan manya-manyan Falasdinawa da shugabannin kungiyoyinsu na qwagwarmayar kwato ‘yanci.
Ko a rikicin nan na baya-baya ta yi ikirarin kashe wasu shugabannin kungiyar Hamas, da kuma yara kanana a wani mataki na dabarar yaki.