✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutumin da ya kera kofar Dakin Ka’aba ya rasu

Shekera 43 ana amfani da kofar Ka’aba da Muneer Al Jundi ya kera daga tataccen zinare

Allah Ya yi wa mutumin da ya tsara ya kuma jagoranci kera kofar Dakin Ka’aba, Muneer Al-Jundi, rasuwa.

Hukumar Gudanarwar Masallacin Haramin Makkah ta ce Muneer da asalin kasar Syria ya rasu ne a birnin Stuttgart na kasar Jamus ranar Laraba.

Masallacin Harami ya yi addu’a Allah Ya jikan Muneer wanda a yanzu haka sunasa ke rubuce a jikink kofar Ka’aba; Allah Ya rahamshe shi.

Abin da aka rubuta a inda ya ka zagaye da jan zane (a hoton kofar Ka’aba) shi ne: Sunan wanda ya yi taswirar Muneer Al Jundi.

Muneer Al Jundi, shi ne injiniyan da ya yi tsawirar sabuwar kofar Ka’abar da aka kera daga tataccen zinare shekaru 44 da suka gabata.

Yadda aka kera sabuwar kofar Ka’aba

Sarkin Saudiyya na wancan lokaci, Khalidi bin Abdul Aziz ne ya zabi Injiniya Muneer ya jagoranci yin sabuwar kofar daga kamfanin Sheikh Mahmud bin Badr.

Muneer injiniya ne a kamfanin Sheikh Mahmud bin Badr a birnin Makkah —kwararru a zayyana da ruwan zinare.

An shafe shekara daya cur (1397-1398 Hijiriyya) kafin a kammala kofar mai nauyin kilogram 280.

An yi kofar ce da zallar ruwan zinare aka kuma kafa ta a dakin Ka’aba a shekarar da ta biyo baya (1399 Hijiriyya).

Sarki Khalid bin Abdul Aziz ya ba wa marigayi Muneer aikin sabunta kofar Ka’aba ne a shekarun 1970 bayan wadda aka yi a zamanin Sarkin Abdul Aziz ta yi rauni.

Bayan kera kofar, an karrama marigayi injiniya Muneer ta hanyar rubuta sunansa a jikin sabuwar kofar wadda yanzu shekara 43 ana amfani da ita.

A lokacin ne kuma Sarki Khalid ya bayar da aikin yin wa Ka’abah sabuwar kofa a cikin ka’abar wadda za ta hade da matakalar da ke kaiwa zuwa rufin Ka’aba.