Duniya dai a koda yaushe tana cike da abubuwan ban mamaki da kuma ta’ajibi.
A nan kuma wani mutum ne mai suna Mista Jonathan Lee Riches, wanda ya yi kaurin suna wajen maka mutane a kotu, sakamakon wani abu da suka yi masa; ciki kuwa da har mahaifiyar da haife shi.
- Yadda rasuwar Bankaura ta girgiza Kannywood
- 2023: Yadda za a fafata yakin neman kuri’un ’yan Najeriya miliyan 84
Jonathan har mahaifiyarsa ya shigar da kara a Kotu, inda ya fada wa kotu cewa, mahaifiyar tasa ba ta ba shi kulawa yadda ya kamata ba, wanda a karshe dai Mista Jonathan ya samu nasara a kan mahaifiyar tasa, inda kotu ta umarce ta da ta biya shi kudi Dala $20,000.
Bayan wannan nasara da ya yi, Mista Jonathan ya sake shigar da amininsa, da makocinsa da wasu daga cikin ‘yan uwansa, har da ma budurwarsa da kuma wasu ‘ yan sanda, sannan ya shigar da karar wani.
Hakazalika, ya maka wani kamfani a kotu da tsohon shugaban Kasar Amuruka, George Bush, kuma duk ya samu nasara a kan kowace kara da kai kotu.
A takaice dai ya shigar da kara sau 2600.
Daga baya an sa sunan Mista Jonathan Lee a matsayin wanda ya fi kowa shigar da kara a kundin tarihi na duniya (World Guinness Book Record), wanda ganin sunansa a cikin wannan kundi ya sa Mista Jonathan ya shigar da karar Guinness Book of Record gaban kotu bisa rubuta rayuwarsa a cikin kundin ba tare sahalewar sa ba.
Ya kuma samu nasara a kotun da kudi har Dala $8,000.000.
Bayan samun wannan nasara ne wani gidan talabijin ya nemi Mista Jonathan domin tattaunawa ta musamman da shi.
A yayin tattaunawar, an tambaye shi me ya sa yake rayuwa shi kadai ba shi da masoyi ko daya?
Nan take ya yi dariya ya mike tsaye ya fice daga dakin shirye-shiryen, bai tsaya ko‘ina ba sai ya yi wa kotu tsinke, inda ya shigar da karar gidan talabijin din bisa cin mutuncinsa a kan yi masa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa domin tozarta shi.
Nan ma kotu ta ci tarar gidan talabijin din Dala $50,000.