Wani mutum da shi kadai ya rage daga kabilarsa, kuma ya rayu shi kadai tsawon shekara 25 a kasar Brazil, ya mutu..
Wata kungiyar kare hakkin ‘yan kasar ce ta bayyana hakan a ranar Lititnin.
- Zulum ya mayar da yara 7,000 da Boko Haram ta raba da muhallansu makaranta
- An tsinci gawar daliban jami’ar Kwara 2 tsirara a daki
Wata hukumar kidayar kabilun kasar Brazil din da aka dora wa alhakin lura da shi, ta ce an tsinci gawarsa ne a kan gadonsa.
Marigayin, mai suna Indio Tanaru, wanda aka fi sani da Tanarun Rami, shi ne mutum na karshe da ya rage daga kabilar da ya fito, kuma tilo da ke zaune unguwar Tanaru da ke jihar Rondonia a kasar.
Haka zalika kafin mutuwarsa shi ne mutumin da ya fi kowa kadaici a duniya.
‘Yan gwagwarmaya a kasar dai sun ce sauran mutane kabilarsa sun kare ne bayan makiyaya sun karkashe su a shekarar 1970-80, yayin da suke kokarin fadada matsugunansu a kasar.