Wani mutum da ya fara tattaki daga kasar Ingila zuwa birnin Makkah na kasar Saudiyya don gudanar da Aikin Hajji yanzu ya kai birnin Silivri na kasar Turkiyya.
Mutumin, mai suna Adam Muhammad dai ya bar Ingila ne a watan Agustan 2021, kuma ya yi wa tafiyar lakabi da ‘tattakin zaman lafiya’.
- Za a kammala aikin titin Kano zuwa Abuja kafin Buhari ya bar mulki – Fashola
- An kama alkama mai guba da ake sayarwa don ci a Gombe
Direbobi dai a kan hanyar na taimaka wa Adam din, kuma yanzu yana tattakin ne tare da wani kare, wanda ya fara binsa daga kasar Serbia.
Adam, wanda dan asalin Iraki ne da ya shafe shekara 25 a Ingila, ya sha alwashin cewa komai wuya sai ya dangana da kasa mai tsarkin don sauke farali.
Yana dai sa ran isa Saudiyyar ne kafin nan da lokacin Aikin Hajji mai zuwa, kuma zai bi ta kasashen Turkiyya da Syria da kuma Jordan.
Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu a kan tattakin nasa, Adam ya ce, “Na fara tattakin nan ne ranar daya ga watan Agustan bara, ina sa ran kammala shi kafin lokacin Aikin Hajji mai zuwa.
“Ina fatan yin ilahirin tafiyar a kafa, akwai abin da yake karfafa min gwiwar cewa zan iya cimma burin nawa, kuma ba gudu babu ja da baya a kansa,” inji Adam Muhammad.
Ya kuma ce sai da ya shafe kimanin wata biyu yana shirye-shiryen tafiyar, sannan ya samu tallafi daga wata kungiya a Birtaniya.
Adam dai ba shi ne mutum na farko da ya yi tattaki daga Ingila zuwa Makkah ba.
Ko a shekarar 2020 sai da wani mai suna Farid Feyadi ya yi irin wannan tattakin domin karyata irin kallon da kafafen yada labarai na kasashen Yamma ke yi wa addinin Musulunci.