A cikin shekara 12 da suka gabata, wani kwararren dan wasan kwaikwayo a kasar China mai suna Lu Jingang ya kasance yana rayuwa ta hanyar kwaikwayon wani matalaucin mabaraci a wani waje mai ban sha’awa tare da barar kudi da abinci daga hannun ’yan kasar.
Ganin Lu Jingang a bakin aikinsa, za a yi tunanin shi ba komai ba ne illa mabaracin da ke neman samun abin biyan bukata, amma hakan ya faru ne kawai domin ya kware a aikinsa.
- NDLEA ta ƙone gonar tabar wiwi a Edo
- Ina cikin takaici kan irin abincin azumi da ake raba wa Kanawa — Gwamnan Kano
Lu kwararren mai wasan kwaikwayo ne wanda ya shafe shekara 12 yana taka rawar mabarata a filin wasan kwaikwayo na Lambun Kinming Shanghe da ke Lardin Henan na kasar China.
Da fuskarsa a lullube, yana kwaikwayon yanayin bakin ciki da tufafi masu kyau, yana nuna fasaharsa ga ’yan yawon bude-ido su cire wani abu daga aljihunsu su taimake shi.
Shi kadai ya kware wajen yin kama da talaka domin a fili sai a ga shi ba wani abu bane illa talakan.
An ba da rahoton cewa, kwararren dan wasan kwaikwayon yana samun Dalar Amurka 9,730 (kimanin Naira miliyan 15 da dubu 512 da 928 da kwabo 20 a kowane wata tare da samun abincin da ba ya tsammanin samu.
A cewar kafar Time Doctor, matsakaicin albashin watawata a kasar China ya kai Yuan 29,000 (kimanin Dalar Amurka 4,000, daidai da Naira miliyan 6 da dubu 377 da 360) wanda ya sa Lu Jingang ya kasance daya daga cikin mutane masu samun kudin shiga mafi girma a kasar ta yankin Asiya.
Wasu sun kai ga kiransa da mabaraci mafi dukiya a kasar China, amma a zahiri ba haka ba ne, shi kwararren mai wasa ne mai yin bara domin samun riba.
Lu ya ce, ya zabi wannan hanyar sana’a da ba a saba gani ba ne, saboda kawai yana son yin wasan kwaikwayo kuma hakan ya ba shi damar yin hakan, ba tare da ya duba ba wata manufa ba.
Iyalinsa ba su goyi bayansa ba da farko, amma daga bisani suka lamunta, bayan da suka ga cewa yana samun kudi sosai a kowane wata, sai suka samu natsuwa.
Bayan tsawon lokaci kuma Lu Jingang ya saba da aikinsa na yau da kullum da wasan kwaikwayon da ya sanya shi shahara a shafukan Intanet a kwanan nan, ya kara samun kwarin gwiwa wajen jawo hankalin mutane da kudinsu.
Tufafinsa na barkwanci, na nuna bacin rai a fuskarsa , yanayin rokon da yake yi sun sauya kammaninsa da hakan ke sa mutane su ciro kudi don su taimaka masa.
Abin da Lu ke samu a wata-wata ya haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, inda akasari ke nuna kishinsu game da halin da yake ciki.
“Ya fi ni farin ciki, ni ne ainihin mabaraci,” wani ya rubuta.“Ina so in bar aikina in koma mabaraci,” in ji martanin wani.
Wani abin sha’awa, Lu Jingang ya gargadi mutane da kada su zo Lambun Kinming Shanghe don gwada sa’arsu a matsayinsu na mabarata, saboda za su sha wahala wajen horar da kansu, lamarin da ya hadu da shi kafin ya shahara.