✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutumin da aka yi wa dashen zuciyar alade ya mutu

Ya rayu na tsawon wata biyu bayan dashen zuciyar alade.

David Bennett, mutumin nan na farko da aka yi wa dashen zuciyar alade a duniya ya mutu.

Bennett, wanda ke fama da ciwon zuciya da ya kai makura ya rayu na tsawon wata biyu bayan dashen zuciyar alade da aka yi masa a Amurka.

Amma rashin lafiyar ta fara tsananta a kwanakin da suka gabata, kamar yadda likitansa Baltimore ya bayyana.

Ya ce David Bennett mai shekara 57 ya mutu ne a ranar Litinin 8 ga watan Maris.

A watan Janairun da ya gabata ne Aminiya ta ruwaito yadda Bennett da aka yi wa dashen zuciyar alade ya bayyana dalilinsa na amincewa, duk cewa ya san akwai hatsari a tattare da yin hakan.

Likitoci a kasar Amurka ne suka yi nasarar yi wa mutumin mai suna David Bennett mai mai shekara 57 dashen zuciyar alade da aka sauya kwayar halittarta a karon farko a tarihi.

An sanar da hakan bayan likitocin sun kammala aikin dashen zuciyar a Asibitin Koyon Aikin Likita na Jami’ar Marylanda da ke Kasar Amurka.

Karon farko ke nan a tarihi da aka gudanar da irin wannan aiki cikin nasara a wani yunkuri na shawo kan matsalar karancin masu bayar da gudunmawa, domin ceton rayukan masu fama a matsalar zuciya.

Sanarwar da aka fitar ta ce bayan aikin da ya gudana cikin nasara, an kafa sabon tarihi a fannin yi wa dan Adam dashen sassan jikin dabba.

Ta bayyana cewa an yi wa wani mara lafiyan mai suna David Bennett, dashen zuciyar aladen na bayan gwajin da aka yi masa ya nuna jikinsa ba zai iya daukar dashen zuciyar dan Adam ba, saboda wasu cututtuka da ya jima yana fama da su.

Dole na zabi a yi min —Bennett

A halin yanzu Mista Bennett yana murmurewa kuma ana ci gaba da kula da shi a asibitin tun bayan an kammala aikin tiyatar da aka yi masa.

“Ba ni da wani zabi face in yarda a yi min wannan dashen ko kuma a bari in mutu. Ni kuma so nake in rayu.

“Na san akwai tsabar kasada, amma ba ni da wani zabi da ya wuce hakan,” inji Mista Brennett, kafin a shigar da shi dakin tiyata.

Bayan shafe tsawon watanni a kwance a asibiti inda na’ura ke taimaka masa wajen yin numfani ta hanyar kauce wa huhunsa, Bennette ya ce bayan tiyatar: “Ina sa ran nan ba da jimawa ba a sallame ni idan na gama murmurewa.”

Dashen zuciyar alade a jikin dan Adam
Dashen zuciyar alade a jikin dan Adam.

Likitan da ya gudanar a aikin tiyatar, Bartley Griffith, ya ce, “Wannan babban tarihi ne a fannin aikin tiyata kuma yana gab da magance matsalar karancin sassan jiki.

“Muna tafiya, sannu a hankali, amma muna da kyakkyawan fata cewa wannan aikin da shi ne irinsa na farko a duniya zai bayar da sabon zabi ga marasa lafiya a nan gaba.”

Muhammad Mohiuddin, wanda daya ne daga cikin wadanda asuka kafa cibiyar dashen zuciya a asitin koyarwar, ya ce aikin ya gudana ne sakamakon shekaru da aka shafe ana gudanar da bincike, bar aka yi wa goggon biri dashen sassan jikin alade, wanda bayan aikin ya rayu na fiye da wata tara.

“Aikin da ya gudanar cikin nasara ya samar da muhimman bayanai da za su taimaka wa likitoci wajen inganta shi domin ceto rayuka,” a cewarsa.

– Sai da aka yi sauyin kwayoyin halitta 10 –

An samo zuciyar aladen da aka dasa wa Mista Bennett ne daga wani garken aladu da aka yi wa sauyin kwayar halitta.

Kafin dashen, sai da aka katse wasu kwayoyin halitta uku da ke iya sa halittar jikin dan Adam kin karba da kuma aiki da sassan jikin alade.

An kuma katse wata kwayar halittar da ke iya sa tantanin zuciyar aladen yin girma fiye da kima.

Daga nan sai aka dasa wa zuciyar aladen wasu kwayoyin halitta shida da za su sa ya karbi sassan jikin alade ya kuma yi aiki da su.

An gudanar da aikin sauyin kwayar halittar ce a kamfanin fasashar sarrafa tsirrai na Rivivocor da ke yankin Virginia na kasar Amurka.

Kamfanin ne ya samar da aladen da aka yi amfani da a aikin dashen kodar da aka yi wa wani mutum wanda kwanyarsa ta mutu a birnin New York a watan Oktoban 2021.

A yayin da wancan aikin ya kasance na gwaji, inda aka an jona kodar daga wajen jikin mutumin, aikin dashen zuciyar aladen da aka yi wa Brennett na zahiri ne kuma an gudanar da shi ne domin ceton rai.

Kafin a gudanar da aikin sai da aka adana zuciyar aladen a na’urar ajiyar kayan tiyata, aka kuma sa mata wani magajin gwaji da kamfanin sarrafa magunguna na Kiniksa Pharmaceuticals ya samar, tare da wasu makamantan maganin da ake amfani da su wajen rage karfin garkuwar jikin cuziyar.

— Masu bukatar dashen halitta a Amurka

Alkaluman hukumomin Amurka sun nuna kimanin mutum 110,000 ne ke jiran a yi musu dashen zuciya, kuma sama da 6,000 daga cikinsu na rasuwa a duk shekara kafin a kai ga yi musu dashen.

Yawaitar masu wannan bukata ta san likitoci suke aikin amfani da sassan jikin wasu halittu domin dasawa a jikin wasu, wanda aka faro tun a karni na 17.

A farko an fara yi ne aikin ne a 1984, amma kwana 20 kacal jaririn goggon birin da aka yi wa ya rayu, bayan aikin.

A halin yanzu ana yawan amfani da bututun zuciyar alade a jikin dan Adam, kuma ana yi wa mutanen da suka samu kuna a jikin dashen fatar alade.

Ana yawan samun aladun da ake amfani da su domin hakan ne saboda girman jikinsu da saurin girmansu, kasancewar ana yawan kiwon su domin amfani da namansu a Amurka.

A watan Nuwambar bara ce Aminiya ta ruwaito cewa, a karon farko wani kwararre a fannin tiyata a Amurka mai suna Dokta Robert Montgomery ya ce, sun samu nasarar dasa wa wani mutum kodar alade, inda suke fatan hakan zai taimaka wajen kawo karshen karancin taimakon koda da ake samu a wannan lokaci.