An gano mutum na farko da ke dauke da kwayar Omicron na cutar COVID-19 a kasar Saudiyya.
A ranar Laraba hukumomin lafiya na Saudiyya suka gano mai dauke da kwayar cutar, wanda shi ne na farko a yankin kasashen Laraba.
- Kanada ta hana baki daga Najeriya shiga kasarta saboda Omicron
- Daliba ta bude shafin koyar da Lissafi da harshen Hausa
Ma’aikatar lafiya ta kasar ta ce tuni aka killace wanda aka gano da cutar, a yayin da jami’anta suke ci gaba da ba shi kulawa.
Kamfanin dillancin labarai na kasar Saudiyya, SPA ya ambato Hukumar Lafiya ta kasar na cewa an gano kwayar cutar ce a jikin wani dan kasar da ya dawo daga wata kasa a Kudancin Afirka.
Hukumar Lafiyar Saudiyya dai ba ta bayyana kasar da mutumin ya ziyarta ba.
Ko kafin a gano kwayar cutar, Saudiyya ta haramta tafiye-tafiye zuwa wasu kasashen Afirka saboda kauce wa yaduwar kwayar cutar ta Omicron.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) dai ta bayyana Omicron a matsayin abin damuwa, gami da fargabar ta fi sauran nau’ikan cutar COVID-19 saurin yaduwa.