✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum na biyu mafi karfin iko a Koriya ta Arewa ya bace

Mutumin da ake ganin shi ne mutum na biyu mafi karfin iko a kasar Koriya ta Arewa, Bayis Mashal Hwang Pyong-so ya bace daga bainar…

Mutumin da ake ganin shi ne mutum na biyu mafi karfin iko a kasar Koriya ta Arewa, Bayis Mashal Hwang Pyong-so ya bace daga bainar jama’a na tsawon lokaci, inda ake rade-radin yiwuwar gwamnatin kasar ta kashe shi.

An fara bayar da bacewar Bayis Mashal Hwang Pyong-so ne a watan Nuwamba, bayan da hukumar leken asiri ta Koriya ta Kudu ta shaida wa ’yan majalisar dokokin kasar a birnin Seoul cewa an “hukunta” shi ne kan nuna halin rashin “kirki” ga Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un. 

“Idan ta tabbata an kori Hwang daga Jam’iyyar Ma’aikata (Workers’ Party), to yana nufin an kawo karshen harkokin siyasarsa, kila ma har da rayuwarsa, duk da cewa ba a sani ba ko har yanzu yana raye,” inji wata jaridar Koriya ta Kudu.

Rahotanni sun ce an yi wa Mashal Hwang gani na karshe a bainar jama’a ne a ranar 13 ga Oktoba. Sai dai akwai dalilan da za a iya gaskatawa cewa an killace shi ne daga jama’a ba a kashe shi ba, kamar yadda jaridar New York Times, ta ruwaito cewa ba a yi amfani da kalmar kawarwa ko kisa ba a rahoton na sirri.

Jaridar Newsweek, wadda ta ruwaito labarin a farkon wannan mako ta ce, ya taba bacewa daga bainar jama’a a baya, amma bai dauki lokaci kamar na yanzu ba. Hwang ya yi layar zana na mako uku a watan Disamban shekarar 2015, lamarin da wata kafar labarai ta Koriya ta Kudu ta bayyana da cewa saboda dalilai na jinya ne.

Ana tunanin an kashe Mashal Hwang ne saboda dogon lokacin da ya dauka ba a gan shi ba da kuma sunan da Shugaba Kim Jong-un ya yi wajen kawar da jami’an da yake ganin sun ci amanarsa.

Rahotanni sun sha bayyana irin jami’ai da dangin shugaban da aka kashe saboda dalilan da suka hada da yin gyangyadi a lokacin da ake taro, da shugaban ke dauka cin amana ne.

Cikin mutanen da aka kashe har da Bappan Shugaba Kim, wato Janar Jang Song-Thaek, wanda aka bayyana da ya ci amanar kasa.